Daga Imrana Abdullahi
Hajiya Dokta Aminatou Abdoulkarim Muhammad ta bayyana cewa abin da ke faruwa a kasar jamhuriyar Nijar a matsayin abu ne na rashin jin dadi da duk inda dan Nijar yake a fadin duniya baya jin dadinsa ko kadan kuma mun yi Allah wadai da shi.
Dokta Aminatou Abdoulkarim Muhammad, jigo ce yar asalin kasar Nijar da ta dauki aikin taimakon al’umma maza da mata yara da manya ya zama abin da take yi da ke a Najeriya.
Ta yi wannan kiran ne lokacin da take tattaunawa da gidan Talbijin na Rtv Sakkwato inda ta ce hakika sun shiga cikin rashin jindadi abin da ke faruwa a Nijar.
Sabida abu ne da ya faru a Nijar amma ya shafi dukkan kasashen Afirka baki daya don haka ba mu jidadinsa ba kuma mun yi Allah wadai da shi.
” Abin da muke bukata a yanzu daga hukumomin duniya shi ne a kawo agaji domin duk abin da ya shafi wata kasa guda daya a Afirka ya shafi dukkan kasashen Afirka baki daya kenan.
Saboda haka muke yin kira da kada a bari sojoji su ci gaba da yin irin wannan kasancewar a halin yanzu ana yin mulkin Dimokuradiyya ne ta yaya sojoji za su rika yin hakan a tsarin Dimokuradiyya kuma kenan ba tabbas na Dimokuradiyya, ai bai ma kamata ace wadanda Gwamnati ta ba su horo da tufafi tare da yi masu komai ba amma su rika yin irin wannan sabanin tsaron yan kasa da aka Sani shi ne aikin su sai su koma suna yaki da yan kasa.
” Mun kira ga daukacin kasashen Afirka da kowa ya kama su Sanya hannunsu a samu gyara a wannan lamarin”, inji Dokta Aminatou Abdoulkarim Muhammad.