Home / Kasashen Waje / Sojojin Nijar Sun Gargadi Kungiyar ECOWA

Sojojin Nijar Sun Gargadi Kungiyar ECOWA

Gwamnatin mulkin soja a kasar jamhuriyar Nijar ta gargadi kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, ECOWAS kan tura sojojinta zuwa Nijar.

Gwamnatin mulkin sojan dai ta sake fitar da wata sanarwa inda ta yi kira ga ‘yan kasar a Yamai babban birnin kasar da su fito kan tituna ranar Lahadi daga karfe 7 na safe agogon kasar wato (8 na safe CET) su yi zanga-zangar adawa da kungiyar ECOWAS domin nuna goyon bayansu ga sabon shugabancin sojojin da suka tsare shugaba Bazoum a halin yanzu.

Shugabannin kungiyar ECOWAS na taro a Abuja, babban birnin Najeriya a ranar Lahadi (yau) 30 ga watan Yuli, domin wani taron gaggawa kan kasar ta Nijar, inda sojoji suka yi juyin mulki a farkon makon nan.

Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS mai mambobi 15 na iya dakatar da Nijar daga cibiyoyinta, da katse kasar daga babban bankin yankin da kasuwar hada-hadar kudi, da kuma rufe kan iyakokin kasar.

Tuni dai Faransa da kungiyar EU suka dakatar da tallafin kudi da hadin gwiwar tsaro ga kasar Nijar, Amurka kuma ta ce za ta bi sahun sauran kasashen.

Janar Abdourahamane Tchiani, shugaban dakarun tsaron fadar shugaban kasa mai iko, ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasar Nijar a ranar  Juma’a yayin da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum ke tsare da sojoji na tsawon kwanaki hudu.

“ECOWAS da kasashen duniya za su yi duk abin da zai kare dimokuradiyya da kuma tabbatar da mulkin dimokuradiyya ya ci gaba da samun gindin zama a yankin,” in ji shugaban Najeriya kuma shugaban kungiyar ECOWAS, Bola Tinubu a wata sanarwa a ranar Juma’ar da ta gabata.

A cikin wata sanarwa da aka watsa ta gidan talabijin a daren Asabar, 29 ga watan Yuli, shugabannin sojojin Nijar sun yi gargadi kan duk wani matakin soji da kungiyar ECOWAS za ta yi, inda suka ce sojoji a shirye suke su kare kasarsu ta haihuwa.

“Manufar taron (ECOWAS) ita ce amincewa da wani shiri na cin zarafi ga Nijar ta hanyar shiga tsakani na soji a Yamai tare da hadin gwiwar wasu kasashen Afirka da ba mambobin ECOWAS ba, da kuma wasu kasashen yammacin duniya,” in ji kakakin mulkin sojan kasar Kanar Amadou Abdramane.

sai dai Majalisar mulkin soji a Nijar ta gargadi shugabannin kasashen yammacin Afirka da ke taro a Abuja kan tsoma bakin soji a juyin mulkin da ake yi a kasar
Nijar na cikin kasashen da suka fi talauci a duniya kuma tana samun kusan dala biliyan biyu (€1.8bn) a duk shekara a matsayin taimakon raya kasa a hukumance, a cewar bankin duniya.

About andiya

Check Also

Return Our Property, Documents In Your Possession, SWAN Tells Ex-President Sirawo

    The Sports Writers Association of Nigeria (SWAN) has warned its erstwhile National President, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.