Home / News / Ba Sabon Bashi Buhari Ya Aiko wa Majalisa Ba – Yahya Abdullahi

Ba Sabon Bashi Buhari Ya Aiko wa Majalisa Ba – Yahya Abdullahi

Mustapha Imrana Abdullahi
Sanata Yahya Abdullahi shugaban masu rinjaye ne a majalisar dattawan Najeriya ya yi wa duniya karin bayanin halin da ake ciki game da takardar karin bayani da Buhari ya aike masu a majalisar.
Sanata Yahya Abdullahi ya ce hakika ba sabon bashi Buhari ya aiko mana ya na son a sake ciyo wa ba.
“Majalisa ce ta nemi ayi mata karin bayani a kan yadda kowa ne bashi yake da ake son yin amfani da shi domin cike gibin kasafin kudin shekara 2018 zuwa 2021, amma ba batun sabon bashi ba ne”, inji Sanata Yahya.
Ya kara da cewa daman can majalisa ce ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi mata karin bayani irin yadda kowa ne bashi yake na Jihohi da kuma na Gwamnatin tarayya da kuma irin yadda za a yi aiki da yawan kudin tare da dukkan wata yarjejeniyar da aka yi kafin wadanda za su bayar da bashin suka gindaya a kan kowa ne bashi.
Sabanin irin yadda wadansu mutane ke yadawa a yanar Gizo cewa shugaba Buhari ya aikewa majalisar dokoki neman a bashi damar cin wani bashi.
Sanata Yahya Abdullahi ya ce neman katin bayani majalisar ta yi kuma shi aka kawo mata dalla dalla kuma majalisar ta mika takardun karin bayani ga kwamitin kula da harkokin batun ciyo bashi a kasashen waje domin su aiwatar da aiki kamar yadda dokar majalisar ta tanadar.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.