Home / KUNGIYOYI / Ba Za Mu Aminta Da Ɗauke Babban Bankin Ƙasar Nan Zuwa Legas Ba -Matasan Arewa

Ba Za Mu Aminta Da Ɗauke Babban Bankin Ƙasar Nan Zuwa Legas Ba -Matasan Arewa

 

Daga Imrana Abdullahi

A farkon makon nan ne haɗaɗɗiyar Ƙungiyar matasan Arewa, wacce ta haɗa ƙungiyoyi 16 daga sassan jihohin Arewacin ƙasar nan suka gudanar da wani taron manema labarai a Kaduna domin su nuna rashin amincewar su da take-taken gwamnatin Tinubu na mayar da wasu muhimman sassan babban bankin Nijeriya daga Abuja zuwa Legas.

Taron, wanda ya gudana a ɗakin taro na gidan Sardauna da ke Arewa House, Shugaban tawagar ƙungiyoyin, Malam Murtala Abubakar ne ya jagoranta, inda ya bayyana cewa “A yau mun haɗa ku a nan ne domin mu nuna adawar mu da damuwar mu kan shawarar mayar da wasu muhimman sassa guda biyar na Babban Bankin Nijeriya (CBN) daga Abuja zuwa Legas.

“Da kuma batun mayar da hedikwatar hukumar kula da filayen jiragen sama ta tarayya (FAAN) da

ma’aikatar sufurin jiragen sama ta tarayya ta yi daga Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya zuwa Legas.”

Daga nan sai Malam Murtala ya ce, “Mu, ƙungiyoyin matasan Arewacin Nijeriya, muna wakiltar murya da muradun miliyoyin matasa daga yankin Arewacin ƙasar nan, waɗanda wannan shawarar ta shafa. Mun yi imanin cewa ba kawai ayyukan rashin gaskiya ba ne, har ma da illa ga ci gaban tattalin arziki, zamantakewa da siyasa na yankin Arewa da ma ƙasar
baki ɗaya.

Ya ce, suna wannan magana ce saboda zanman su al’umma masu da’awar haɗin kan ‘yan ƙasa, da zaman lafiya, tare da ci gaban wannan ƙasa mai albarka, inda suka ce tun farko ma dai, babban bankin ba shi da hurumin ɗaukar wannan mataki, musamman bisa la’akari da dokar da ta kafa Babban birnin tarayyar.

Da ya ke tsokaci game da sassan masu muhimmanci da Babban bankin zai ɗauke zuwa Legas kuwa, Malam Murtala cewa ya yi, “Muna tambayar dalilan da ya sa Babban Bankin ƙasa ɗaukar wannan mataki a kan muhimman sassan ta biyar, waɗanda suka hada da sashen Kula da Harkokin Bankuna; Sashen Kula da Sauran Cibiyoyin Hada-hadar Kuɗi; Sashen Kula da Buƙatun Masu hulɗa da Bankuna; Sashen Tsarin Sarrafa Biyan Kuɗaɗe da Sashen Dokokin Hada-hadar

Kuɗi.”

Babban Bankin ya kawo hujjar ɗaukar wannan taki komawa Legas, inda ya ce

ya ɗauki wannan tsari ne domin rage cunkoso a babban ofishin sa da ke Abuja, wanda aka gina domin ma’aikata 3,000, amma yanzu yana da 4,000.

To, amma sai dai Matasan sun yi nuni da cewa wannan dalili ba shi da ƙarfi, domin babban bankin ai zai iya faɗa ofishin nasa a Abuja cikin sauƙi, ko kuma ya raba

ma’aikatan nasa zuwa wasu yankuna, maimakon ya tattara su a Legas.

 

Haɗakar matasan Arewar suka ce, mayar da waɗannan manyan sassa guda 5 zuwa Legas zai haifar da mummunar illa ga hada-hadar kuɗi, kwanciyar hankali da tsaron ƙasar nan, wanda hakan zai haifar da tazara tsakanin Babban Bankin ƙasa da gwamnatin tarayya mai hedkwata a Abuja, da kuma kawo cikas ga daidaito da sadarwa a tsakanin su.

“Haka zai rage wa cibiyoyin hada-hadar kuɗi da kwastomomi na sauran yankunan ƙasar nan,

musamman Arewa, wacce tuni ta ke fama da ƙarancin cibiyoyin hada-hadar kuɗi.

Ƙorafi da koken matasan Arewar, ba a Babban Bankin kaɗai ya tsaya ba, sun kuma yi tofin Allah-tsine ga Ma’aikatar Sufurin Jiragen

Sama ta Tarayya bisa matakin da ta ɗauka na mayar da hedkwatar Hukumar Kula da

Filayen Jiragen Sama na FAAN zuwa Legas, “Wanda hakan ya saɓa wa ƙa’idar ɗa’a ta

tarayya da ke cikin Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya,” in ji matasa.

Suka ce, “Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama dai Hukuma ce mai kula da kuma gudanar

da dukkan filayen tashi da saukar jiragen sama na ƙasar nan, ba wai na Legas kaɗai ba. Saboda haka, ta hanyar mayar da hedkwatarta zuwa Legas, FAAN na lalata tsarin tarayya na ƙasar nan da kuma tsarin wakilci na daidaito da shigar da

dukkan jihohi da yankuna a harkokin mulki da gudanar da mulkin ƙasar.

“Hakan kuma zai haifar da mummunar illa ga tsaro da ingancin filayen jiragen sama a sauran sassan ƙasar nan, musamman Arewa, waɗanda tuni ke fuskantar ƙalubale na rashin cikakken kulawa, da kashe masu kuɗi da rashin cikakken amfani da su.”

A ƙarshe, matasan sun jawo hankalin gwamnati da cewa, “Don haka muna buƙatar gwamnatin tarayya ta janye waɗannan matakan da Babban Bankin ƙasa da Hukumar Kula da Filayen Jiragen

Sama suka ɗauka cikin gaggawa, sannan ta dawo da martabar Abuja, Babban Birnin Tarayya.

An zabi Abuja ne a matsayin babban birnin ƙasar

nan don zamowar ta a tsaka-tsaki ga jinsunan da yankunan kasar. Har ila yau, Abuja tana taimaka wa wajen daidaitawa ga yankuna da sassa daban-daban na

kasar nan.

“Saboda haka in gwamnati ta mayar da manyan sassa 5 na Babban Bankin ƙasa da hedikwatar

Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama zuwa Legas, to ba wai kawai rashin mutunta zaɓi da hangen nesa na waɗanda suka kafa

Abuja ba ne, har ma da haifar da ƙyama a tsakanin al’ummar yankin Arewa da sauran yankuna, waɗanda ba su da wakilci a Legas.

Ƙungiyoyin da suka haɗu a wannan taro, sun haɗa da ‘Arewa Defense League,  Association of Northern Nigerian Students, Arewa Youth for Development and National Unity, Arewa Young Women’s Rights Advocate Council, Northern Youth in Defense of Democracy, Arewa Radio and Television Commentators, Northern Youth Democratic Agenda

Da kuma The Time is Now, the Time is Ours Association.’

Sauran sun haɗa da ‘Arewa Youth Advocate for Peace and Unity Initiative, Northeast Youth Artisans Association, Bauchi State Citizens Action for Chang, Youth Initiative for Good Governance, Coalition of Tiv Youth Organization, Matasan Arewa Ina Mafita Development Association, Toro Youth Circle da Northern Youth Coalition Forum.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.