Home / KUNGIYOYI / BA ZAMU AMINCE DA CIN MUTUNCIN YAN AREWA A JIHAR ONDO BA – SHATTIMA YERIMA

BA ZAMU AMINCE DA CIN MUTUNCIN YAN AREWA A JIHAR ONDO BA – SHATTIMA YERIMA

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
Kungiyar matasa masu tuntuba ta arewacin Najeriya (AYCF) ta gargadi Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredelu “bisa iron yadda a kwanan nan aka rika gallazawa yan Arewa a Jihar”.
  Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun shugaban kungiyar na kasa  kwamared Shattima Yerima, inda ya ankarar da Gwamnan a cikin takardar cewa ya dace fa Gwamnan ya duba sosai da idanun basira irin yadda lamura ke faruwa ga yan Arewa a Jihar ta Ondo.musamman yadda yayan kungiyar Amotekun ke kama wa tare da tsare yan Arewa da ke gudanar da harkokinsu a cikin Jihar.

Kungiyar tuntuba ta AYCF a cikin takardar da ta raba wa manema labarai ta kalubalanci irin yadda lamarin ke faruwa, abin da kungiyar ta bayyana da cewa “wadansu mutane dauke da makamai da suke labewa tamkar su jami’an tsaro ne kuma a cikin kasar da akwai jami’an Yan Sanda, da Yan sandan farin kaya na DSS da kuma jami’an tsaron farin kaya na NSCDC, da sauransu wadanda su ne kawai ke kunshe a cikin dokar kasa da aka amincewa su yi aiki bisa dokar kasa”.

Kungiyar sai ta ci gaba da cewa ” muna aikawa da gargadi da kakkausar murya ga Gwamnatin Jihar Ondo da su daina rufe idanuwan ta a game da irin yadda ake kaiwa yan Arewa hari duk da cewa yan Najeriya ne masu cikakken yanci da suke gudanar da harkokinsu na saye da Sayarwa da ayyukan da dokar kasa ta amince da su ayi a cikin jihar”.

Ya dace Gwamna, Gwamnati da jama’ar Jihar Ondo su Sani cewa “idan sauran al’ummar yankin arewacin Najeriya sun dauki irin wannan matakin na cin mutunci, matsin lamba ga yan asalin Jihar Ondo, da a yanzu ba za a samu wani dan asalin Jihar Ondo ya na zaune a arewacin Najeriya ba, ko ya na zaune ko kuma ya rika gudanar da harkokin kasuwanci”, inji Shattima Yerima shugaban Gwagwarmaya.

” saboda haka ya dace Gwamnan ya dauki matakan da ya dace”.

Kungiyar AYCF sai ta fayyace karara a fili cewa; “mun gashi da irin wannan wulakanci da cin mutuncin da ake yi wa jama’ar Arewa a Jihar Ondo don haka kamar yadda muka bayyana yin da farko muna bukatar Gwamna ya dauki matakan kawo karshen wannan lamarin kowa ya samu kwanciyar hankali da walwala cikin lumana”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.