Home / News / CI GABAN NAJERIYA SAI MUN GYARA HALAYEN MU DA RIKE GASKIYA DA AMANA – INJINIYA KAILANI

CI GABAN NAJERIYA SAI MUN GYARA HALAYEN MU DA RIKE GASKIYA DA AMANA – INJINIYA KAILANI

SAKAMAKON ZARGE ZARGEN DA DIMBIN JAMA’A SUKE YI DAGA BANGAREN HAGU DA DAMA A KAN BATUN SHIGOWA DA GURBATACCEN MAI DAGA KASAR “BELGIUM” ZUWA NAJERIYA, INDA HAR YA KAI GA WASU NA ZARGIN CEWA ANA SON A RUFAWA WADANDA SUKA AIKATA WANNAN AIKIN NE SABODA ANA GUDUN KADA WADANDA SUKA SAMU MATSALAR SU TASHI A TUTAR BABU.

Hakan ta Sanya gidan rediyon tarayya na Kaduna ya shirya wani shirin tattaunawa da masana inda aka kira Injiniya Dokta Kailani Muhammad masani a kan harkokin man fetur da kuma Alhaji Bashir Dan Malam shugaban shiyya a Kungiyar Dillalan man fetur ta kasa wato “IPMAN” inda suka tattauna tsawon sama  da awa biyu aka ba jama’a damar su bugo waya domin yin tambaya, karin bayani da nufin samo hanyoyin warware bakin zaren.

Malam Yusuf Zaini Dogare daya daga cikin masu jagorancin shirin ya fara da yin shimfida game da wasu Zarge zargen da aka yi kan batun yadda man fetur ya gurbace har aka bari ya shigo cikin gidajen mai al’umma suka fara saye suna yin amfani da shi wanda sanadiyyar hakan wasu suka dan yi asarar lalacewar ababen hawansu. MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI,Ya rubuta wannan tattaunawar domin amfanin jama’a a ciki da wajen Najeriya da duniya baki daya.

Ga dai yadda tattaunawar ta kasance;

INJINIYA Kailani Muhammad tsohon ma’aikacin matatar mai ta Kaduna ya bayyana cewa dole sai kowa ya gyara halinsa domin a samu ci gaban Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a cikin wani shirin gidan rediyon tarayya na Kaduna game da batun da ake fama da shi a yanzu na shigo da gurbataccen man fetur da ke lalata Injunan ababen hawa da sauran Injunan da ake zuba masu man fetur.

Injiniya Kailani Muhammad wanda tsohon ma’aikaci ne a matatar man fetur ta Kaduna, ya bayyana cewa kamar matatar ta Kaduna ta na da tsawon wa’adin yin aiki ne na tsawon shekaru Dari, amma a yanzu ta  yi aikin shekaru Arba’in ne (40) kawai.

Ya ci gaba da bayanin cewa abin da muka fuskanta a da can baya na rufe matatar da kuma wurin ajiyar mai da dangoginsa (Daffo) shi ne abin da ke faruwa dole sai mun gyara halayen mu tukunna, duk a inda mutum yake ya rike gaskiya da amana.

Injiniya Kailani, ya bayar da misalin cewa a shekarun baya can lokacin ya na shugabancin ma’aikata a matatar mai matakin da ya dauka na rufe matatar man, ya aikata hakan ne sakamakon irin matsalar man fetur da aka kawo a Najeriya da ta Sanya mutane na mutuwa a kan layin neman man fetur a gidajen mai halin da ya Jefa dukkan al’ummar kasa a cikin wani yanayi.

Kailani, ya kara da cewa ” a lokacin an bayar da kwanciyar gyaran matatar mai amma sai aka ba kamfanin Total, alhalin kamfanin Total ba aikin Injiniya yake yi ba wato aikin gyare gyare, kamar yadda kowa ya Sani kamfanin Ciyola ne ya gina matatar mai ta Kaduna kuma akwai lokacin da ake daukar kwanaki 43, ana aikin gyare gyaren matatar daga aikin gyaran ruwa zuwa aikin gyaran babbar na’urar sanyaya wa da ke aiki a matatar da yanki na daya da na biyu wurin da ake daukar albarkatun man da aka tace baki daya sai dauka a kai inda za a yi amfani da su”.

“Amma sai aka dauki aikin aka ba kamfanin Total kuma ba su iya yin aiki ba, sai aka ce mana mu injiniyoyin da sauran ma’aikatan dauke gudanar da gyare gyare sai aka ce mana kada mu ta ba, har aka wayi gari aka yi shekara daya suka kasa yin aikin, sai dole aka zo aka yi amfani da mutanen da ke aiki a cikin gidan, abin da ya faru a lokacin shi ne idan aka ce a canza kayan da ke aiki a Injunan sai a gyara madadin a canza su baki daya wannan aka yi fama da shi a shekarar 1998 don haka abin da aka gyara ba zai yi aiki ba.

Amma a can baya idan an yi aikin yin gyara da canza abubuwan da ya dace a canza na tsawon kwanaki 43  zamu tayar da matatar mai domin wadannan kwanaki uku din shi ne ana yin su ne ba wuta a ko’ina baki daya.

In dai za a yi gyara ne domin Allah matatar mai za a iya tayar da ita ta yi aiki shekaru biyu sannan sai kuma a sake Dakatar da ita ayi wani aikin gyaran kuma.

Tsawon shekaru da yawa ake kokarin kamfanin NNPC  ya rika cin gashin kansa ba a samu ba sai yanzu lokacin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari , an bayar da aikin matatar Fatakwal da za ta rika fitar da litar mai miliyan sha daya  har an kawo kayayyaki an kammala aikin duba wa sarai don haka idan mutum zai yi magana ya bari sai ya san abin kafin ya yi magana a kai.

Kuma tun da a halin yanzu muna da wasu shekaru Sittin  (60) da matatun man za su yi aiki  ga shi kuma an ba wasu lasisin yin kananan matatun mai sun kasa yi.

Saboda haka in har ba yabawa wannan Gwamnatin ba to ” mun zama butulu, shekaru biyu da rabi da ya gabata an samu layin mai a kaar nan? da a lokacin kirsimati akwai miyagu da suke shirya makirci a kasar nan sai ka ga layi a gidajen mai, amma a wannan karon tun da sababbin shugabannin gudanarwa suka zo, a tsawon shekaru biyu da rabi ba a ta ba shigowa da gurbataccen mai ba. Kamar yadda wani shugaba a harkar mai ya yi bayani a bangaren yin lodi mai da  aka dauko wadannan Jiragen mai akwai kuskuren da aka samu , domin an yi Gwajin man nan a dakin Gwajin da suke da shi aka ce komai ya yi dai dai har aka shigo da man cikin Najeriya. Kuma akwai kamfanoni guda hudu da aikinsu ne suga cewa man da aka shigo da shi lallai ya cika duk wata ka’idar da ya dace a cika ta nagartar man kuma sun bayar da takarda cewa ya yi, to, amma abin da ke ba kowa mamaki shi ne sinadarin da aka gani a cikin man fetur ta yaya ne?

“Domin ni na gaya masu cewa akwai zagon kasa tun da an samu wannan sinadarin da bai kamata a samu a cikin man fetur ba har da zai bayar da matsala, kuma shi Alhaji Faruk da yake yin wannan magana na kudi biliyan dari da sha bakawai domin a gyara wannan mai da wani man mai kyau, ai wadancan hukumomin da na fadi a baya da ke da aikin tabbatar da cewa man nan lafiya kalau yake, yakamata azo a yanzu a hadu a gudanar da bincike aga ta ina aka samar da wannan sinadarin itanol a cikin man fetur.

Domin ai ana duba wasu abubuwa ne da suka hada da inganci sosai har kashi Casa’in da daya, amma mu na ganin wasu ne ke ganin sabuwar Gwamnati ta shigo a matatar mai NNPC domin akwai wadanda aka sallama daga hukumar DPR akwai kuma wadanda suka so yin juyin mulki a NNPC a yanzu su na nan a waje duk ba su jin dadi.

Game da binciken da shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarni ayi bincike shin ta yaya za a yi binciken tun da dai kamfanin NNPC ne ke shigowa da mai Najeriya.

Sai Injiniya Kailani ya ce “ai a halin yanzu an ce hukumar gudanarwar NNPC ta zo ta yi bayani kaga binciken farko kenan, kuma kamar abin da nake fadi ne kamfanoni hudu duk sun gudanar da aikinsu kuma sun bayar da tabbacin cewa ba wata matsala a cikin man nan to, masu magana a kafafen Sada zumunta na zamani cewa a cire wane a cire wane shin me ya kawo batun cire wane a yanzu.

Injiniya Kailani ya kara da cewa akwai batunbda wasu ke yadawa a kafafen Sada zuminta na zamani savage kira soshiyal mediya, wasu na gani Muhammadu Buhari ya sauka a matsayinsa na babban ministan man fetur na kasa.

Kuma ai wasu na ganin cewa ma me yasa aka Gina matatar mai a Kaduna bayan a Arewa ba man fetur, to, Gyada da Auduga fa da aka gina.

Ai a yanzu Buhari ya zo da wani tsari inda man Kulomari, yankin Chadi da wani wuri kuma duk an samu man fetur mai yawan da za a iya hako shi har a sayar.

Kuma wasu na ta zage zagen cewa me yasa ba mu da Iskar Gas amma aka ce a kawo bututun Gas daga Ajkuta, Kaduna da Kano, don haka muna fatan Allah ya sa kafin shekarar 2023 din nan an aiwatar da shi domin zai bayar da damar kamfanonin mu duk su tashi jama’a su samu ayyukan yi da yawa.

Akwai Iskar Gas na yin Girki akwai kuma na wanda kamfanoni za su yi amfani da shi a rika sarrafa abubuwa da dama.

Na kulomari an tabbatar da cewa Iskar Gas yawanta ya kai Tiriliyon da yawa a kwance a wurin kasar Bauchi saboda haka idan ma sun toshe kamar yadda suka ce in an gama ma za su toshe ai karya suke yi.

A ta bakin wani mai sana’ar sayar da man fetur, a cikin tattaunawar hannu da yawa ya ce su ne masu Motoci da gidajen mai, don haka idan an dauki misalin gidajen man da aka fi shan mai a arewacin Najeriya kuma a wane Jihohi ne misali Kano,Abuja, Kaduna da wani bangaren Adamawa to idan aka dauki Jihar Kano kanta da aka fi zuzuta wannan al’amarin zaka ga man da ya shiga al’umma bai wuce mota biyu ba zuwa uku kuma man ya KASU kala uku akwai wanda zaka gan shi baki, akwai wanda zaka gan shi kamar ruwa da kuma wani mai dallaki dallaki saboda haka daman can an je dakin Gwaje gwajen mai an kuma duba,amma idan ana maganar sai kaga kamar duniya za ta tashi.

Kaduna kuma mota daya ce kawai ta shiga saboda haka domin Allah jama’a su yi wa kansu adalci mutum nawa ne aka gani sun ce suka ce sun sha mai motarsu ta samu matsala?

In ka ce garin Legas akwai bambanci da su matuka domin  motocinsu 3620 Duke dauka mu kuma motocin mu daga 40, 60 sai abin da ya yi sama. Kuma ko a Abuja a iya binciken da muka yi bai wuce mota biyu ba na wannan mai da ake magana a kansa, amma idan siyasa ta shigo sai ka ji kamar me, da ace na NNPC ya shiga cikin al’umma wanda ya kawo duk da yake ba ita kadai ta kawo ba akwai wasu kamfanonin da suka kawo tun da ba a kammala binciken ba bai kamata in bayyana su ba.

Sai nan take Injiniya Kailani ya ce za a bayyana kamfanonin akwai Oondo.

Sai mai magana ya ce bari in karasa inda ya ci gaba da cewa su da suke sayen mai sun fi sayen na kamfanin NNPC domin ya fi sauki, amma wannan na yan kasuwa ne irinsu da za su sauke a wurin da suke sauke mai don haka akwai bambanci koda yake na NNPC ma da ake magana da nake jin wani na ta magana ya dace a rika sanin lamari kafin a fadi magana tukunna.

Wallahi na kasa gane lamarin domin kamar siyasa ta shigo cikin maganar misali ba ma tushen maganar ba sai an haka rami tukunna sai a daddako maganar baki daya.

Shin wannan lamarin ya shafe ku kun yi asara?

Alhamdulillahi, Asara kala uku ce akwai ta Dakatar da motocin da suka loda sai aka ce su dakata a can. Sai kuma idan mota ta kawo wani garin da za ta sauke kayan misali kamar ka kawo Kaduna sai a tsayar da motar a inda take saboda haka wannan duk asara ce.

 Asara ta biyu shi ne an tsoratar da masu sayen mai.

Ta uku kuma wani haka kawai zai zo ya yi ta magana kuma akwai asarar lokaci da kuma rufe gidajen mai a inda ake ganin an sauke man kaga me zaka cewa ma’aikatan wurin domin wani sai ya je zai samu abin da zai kaiwa iyalansa saboda haka an yi asara amma abin da yasa muke Kaddara asarar irin wannan ba ta kai karshe ba shi ne NNPC ta ce duk a tattaro komai kuma a yanzu kamfanonin da aka sayi kayan a hannunsu sun bayar da fom shin me yasa kamfanin ya bada fom don haka a daina sa siyasa domin mu yan kasuwa ne.

Nan take sai Injiniya Kailani ya ce abin da ya sa ake yin wannan shi ne ni na duba soshiyal midiya sosai suna maganar wai shugaba Muhammadu Buhari ya sauka a matsayinsa na babban minista na mai. Yan kudu sune matsala domin suna cewa me ya sa aka zo aka gina matatar mai a Kaduna ba mu da mai duk irin maganganun da ake yi wasu na cewa shugaba Buhari Bafillatani ne kuma shugaban kamfanin mai na kasa NNPC shima dan Arewa ne duk haka suke ta rubutawa a kafafen soshiyal midiya saboda haka dole ne mutanen Arewa ayi karatun ta natsu domin kasar nan duk ta mu ce. In kuma ma man na su ne da suke gadara ai da kudin gyada da auduga aka tono man kusan Tamanin bisa dari zaka ga rika gani a ko wace kafar labari ana ta zage zage haka kawai.

Amma wannan tsarin sabuwar dokar kamfanin man fetur ta zo da batun mai na Kulomari, yankin Pida  da na yankin Banuwai ai duk bincike ya nuna an samu man da yawan gaske da har za a iya Sayarwa.

Kamar batun AKK din nan duk suna ta zage zage aka ce a kawo Bututun daga Ajakuta, Kaduna zuwa Kano fatan da muke yi shi ne Allah ya sa kafin karshen wannan Gwamnayi a shekarar 2023 an aiwatar da shi, wallahi, duk wata matsalar da muke fuskanta ta rashin wutar lantarki za ta wuce ga kamfanonin masaku, yanzu idan kaje Sharada kamfanoni sun mutu, amma da wannan za a samu wuta sosai da kamfanoni za su yi aiki da ita da kuma Iskar Gas domin dafa abinci.

Idan ana sarrafa abubuwa wasu kamfanoni za su fito saboda haka na yankin kulomari akwai tiriliyan da yawa na iskar Gas a wajen Bauchi idan ma an ga ma Sanya bututun sun toshe kamar yadda suka wallahi karya suke yi.

Akwai wani abin da nake son Alhaji Bashir ya yi magana a kai na san zai yi masu dadi shi ne maganar cire tallafi da Gwamnati ta ce da za ta cure daga watan shida ne ko Bakwai sai ta dawo ta janye batun.

Ta fuskar kungiyar ku shin yaya kuke ganin wannan kwangaba kwan baya da kai kanka fahimtar da kai wa abin?

Bashir: Na farko yana da kyau mutane su san meye tallafin shi ne kamar ka dauko wani abu tallafa Mani in sauke, ko yi Mani kaza ka tallafa Mani na dauko wani abu in sauke.

Yan kasa ya na da su san tallafi shi ne misali Gwamnati na son yan kasa su sha mai da sauki, misali ana Sayo man dari biyu sai Gwamnati ta ce ba za mu sayar maku da shi dari biyu ba za a sayar maku a kan naira dari ka ga akwai naira dari da ake Tallafawa da Gwamnati ke bayarwa.

Na biyu, tun da an tabo yankin Arewa da kudu ana maganar tallafi shin wai ina yake tafiya ne tallafin har yanzu idan ka dauki tsakanin Legas da Ogun su na shan lita miliyan Talatin kaga duk masu yin ihun ashe man dai ya na can a gindinsu kaga su ake ba tallafin wannan kenan.

Abin da yasa da Gwamnatoci da su wadanda ke da alaka da abin suke cewa tallafi tallafi gaskiya ne kudi ne idan an sayar da danyen mai naira Goma sai a dauki naira Takwas sai a saka ayi tallafi kuma kudin su ake ba Gwamnoni da sauran ma’aikatan Gwamnati sai suke ganin cewa sun yi alkawarin za su gina rijiya to ina kudin da ake cewa za a ba su shi ya sa suke son a cure tallafin.

Na hudu kuma mu’amallar my da hukumar NNPC ba ta ba mu dama ba ace an tambaye mu ayi tallafin mai ko kar ayi idan yau Gwamnati ta ce mu dauko wannan man na mu, mu ba mutane kyauta ba ko Kwabo.

Amma idan an dauko mai aka ce ba za a ba mu riba ba to nan ne za a ji bakin mu.

Da aka ce meye ra ayi na, to, da nine kawai na Bashir Ahmad Dan Malam sai in fadi ra’ayi na ba na kungiyar masu sayar da mai masu zaman kansu ba. Amma dokar yadda aka yi yarjejeniyar da Gwamnati mu yan sa idanu ne sai dai zamu iya bayar da shawara a wurin da yakamata.

Shin wai waye ya yo dokar nan ne yan majalisa ne suka yi ta kuma suka ce daga lokaci kaza zuwa kaza idan shugaban kasa ya sa hannu kada a ba NNPC dama idan ta shigo damai to ba batun tallafi, a yanzu ko an Dakatar da shi ai ya zama doka sai a kira yan majalisu da Gwamnoni cewa ba su amince da dokar ba ayi gyaran da za a yi kawai.

Amma idan an ce tallafi shi ne mutane su daina zargin masu gidajen mai ne ke cin tallafin kai da kake zargin mai gidan mai don yau in an cire tallafin me ya sa wasu suka ta so suka ba su yarda ba, an cire tallafin ka ga ba mai gidan mai ba ne ke karba duk kai ne dai kake amfana da shi saboda haka maganar tallafi muna da ta cewa a kansa iyakar inda doka ta ce kuma akwai abin da zamu ko ba zamu ce sai yadda doka ta ba mu dama.

 Injiniya Kailani, ga kari a kan maganarsa

To, amma a minti daya saboda

To tallafi Gwamnati ta na na su mai a naira dari da Arba’in da biyar kaga wannan daga wurin ajiye mai kenan ( Daffo) wannan tsakanin dari da arba’in da biyar zuwa dari da Hamsin da biyar shi ne abin da Gwamnati ke bayarwa. Yanzu NNPC ta zama kamfani mai cin gashin kansa shi ya sa ta ce ita ba za ta iya ba saboda kudin tallafin biliyoyi ne a shekara ya kai tiriliyan daya da wani Digo.

Kamar yadda ya yi maganar Gwamnoni zaman kashe Wanda kawai suke yi sai dai su jira kawai.

To, a yanzu muna tattaunawa ne da shugaban kungiyar Dillalan mai na arewacin Najeriya Alhaji Bashir Ahmad Dan Malam da wani masani  mai yin sharhi a kan albarkatun man fetur Injiniya Kailani Muhammad, to a yanzu zamu baku dama ku buge waya domin tofa albarkacin bakinku.

Mutum na farko da ya fara bugo waya shi ne Ibrahim Alaramma Rigachikun, hakika tattalin arzikin Nijeriya ya ta’alla ne a Kan batun man fetur, tambayata a nan shi ne masana na cewa nan da dan lokaci kadan man fetur din za a neme shi a rasa shin a hasashensu da kungiyarsu yaya ko wace jiha ce yakamata ta koma bayan wannan man?

Sai kuma mai waya na biyu Isma’ila Jafaru Dan Musa, saga Katsina, na farko maganar Injiniya ta nuna mana cewa a rika Sanya mutane a muhallin da suka Sani domin Injiniya Kailani ya tabbatar mana cewa an gina matatar mai domin yin aikin shekaru Dari, amma a yanzu duk shekaru 40 kawai ta yi don haka a rika Sanya komai a muhallinsa.

Sai maganar kungiyar masu sayar da mai masu zaman kansu su su na bayar da mai ai suna daular ma’aikata da yawa misali a Dan Musa akwai gidajen mai biyar.

Mu abin da muke fata shi ne a rika bayar da aiki ga wadanda suka san abin, da fatan za a samu ci gaba, nagode.

Sai mai waya na uku Abubakar Baban Umar Kusfa Zariya, tambaya ta a nan shi ne kamar bayanan da kuka yi sai ya kasance ita Gwamnatin lokaci bayan lokaci idan ta nushadu sai ta ce tallafi ya na nan shin wai da gaske tallafin akwai shi, ina fata za a kara mans haske a kan wannan.

Kabiru mai lantana katsinawa karamar hukumar Soba, tambaya ga shugaban Dillalan mai fetur na arewacin Najeriya, suns kuwa bibiyar gidajen mai su tabbatar su sayar da mai a kan farashi?

Sai Alhaji Bashir Dan Malam, ya fara amsa tambaya cewa na farko a kan mai magana Sama’ila Dan Musa,da alama bai fahimci me ake yi ba ko kila zuciyarsa na wani wurin

Abin da Ogana ya fadi ai duk bayanan kusan dai- dai ne da nawa sai dai shi, na ce misali a da can muna shan mai lita  dubu Talatin amma a yanzu ana shan lita dubu Sittin  kaga mutane sun karu don haka dole masu bukatar mai su karu kwarai.

Na kuma yi magana game da batun cewa matatar mai ta tsufa na ce da dan shekaru 10, da dan 20, 30, 40 da mai Sittin za su yi daya? Koda yake maganar shekaru dari

Akwai kuma maganar Shafi’u, a kan maganar sayar da kayi, shi maganar sayar da mai shi ya sa muke ta tattaunawa saboda matsalar nan da aka samu idan zaka kashe naira dubu Goma sai ka kashe dubu dari, ko a garin Legas akwai yan Iska ko ka ba su kudi ko kuma su fasa maka taya su shiga cikin lungu don haka kawai ka biya ka wuce lafiya.

Na biyu da kake ga ni fa ba jarinsa bane gidan man ne kawai yake da shi. Kuma idan nisa ya yi yawa to nan ma dole ne sai an duba abin da zai kawo maslaha a sayar da mai a wasu wuraren ma sai kaga ga man a gidan mai amma sai dai a rika yin Bacci kawai ba a sayen man, amma da an samu wata yar tangarda ko yaya take kafin man ya dawo dai dai sai fa an yi hakuri kafin daga baya a samu yadda ake so.

A yanzu garin Legas ba mai garin Fatakwal ba mai saboda dakatarwar da aka yi ana son yin gyara sai na ce sai lokacin da ba za a fasa Mani taya ba sannan zan dauko man shin yaya mutumin Kaduna zai yi? Kano da Illela duk za su yi, wallahi wani lokaci kason mutanen Legas ake saye domin a kawo wa jama’a su sha man don haka a dan yi hakuri ayi hakuri komai zai wuce.

Da yake amsa tambaya a game da batun ko akwai tallafin da ake ta magana a kai ko kuma duk dabara ce kawai? Sai Injiniya Dokta Kailani, ya ce a halin yanzu dai kamfanin NNPC ya zama mai cin gashin kansa don haka an kusa bude kasuwa kowa ya shigo da mai.

Saboda haka idan wani ya shigo da na sa ya na Sayarwa naira dari, ina zaka je wurin gidan man wani ca.

Kaga an samu sauki an bude kasuwa, saboda haka shi wannan tallafin da ake magana ba gaibu ba ne akwai shi kuma Gwamnati ce ke bayar da shi.

Sai wani da ya bugo waya mai suna Yusuf Na labahani saga Kano, ya ce hakika shugaba na dilalan mai masu zaman kansu na kokari musamman a Kano saboda shi a kamar yadda ya ce yana sayen mai a wurinsu don haka ya ya ba kokarin da suke yi, ina sayen mai a gidajen mansa kuma farashin na yin kasa da sauran wasu gidajen man da yawa, saboda kan hanyar da nake wucewa ne musamman a gidan mansa na kan hanyar bela,don haka Allah ya sa a ga ma lafiya.

Injiniya Kailani, ya ci gaba da bayanin cewa shawarar da yake ba Dillalai masu zaman kansu shi ne akwai wadanda suke ga manyan wurin ajiyar mai wato (dafot) akwai NARTO, Soja,Yan Sanda, akwai kwastan.

Dole sai Gwamnati ta tashi tsaye ta wargaza su sannan mutanen kasa za su samu sauki domin an bayar da mai a kan farashin naira 145 aka ce a sayar da mai a 165, amma zaka ga wani ya na Sayarwa 180 ko 175 yaje kawai ya murde kan famfansa, wasu kuma da daddare za a sauke man a rika Sayarwa a cikin Jarkoki, wannan ne ya sa tun da farko na ce mu rike gaskiya da Amana sannan mu gyara domin idan ba mu gyara ba akwai matsala.

Kamar yadda na ce ne a gidan rediyo Faransa da na ce a rana ana iya samun yan Jiragen masu satar mai guda Goma su waye duk da tsaron da ake da shi na sojan kasa  da  sama to ta ina suke bi? saboda haka sai mun gyara tukuna.

Kaga a yanzu wani ya buge waya daga Kano ya ce gidan man dan Malam na da kyau to, amma kashi Tamanin duk ba su da kyau.

Sai shima Alhaji Kabiru daga Kano, da farko dai ina yi wa zababben shugaba mai shugabancin Kano,Jigawa da Yobe barka da zuwa kuma mun ji dadin irin yadda ake yi wa jama’a bayanin abin da ke faruwa a harkar mai, saboda haka muke yin kira ga Gwannati da ta duba sosai ta waiwayi lamarin ta na yadda yake

Sai Injiniya Kailani, ya yi maganar cewa shima dan Najeriya ya na da matsala

Suma ma su gabatar da shirin sun ce dama ku da masu bugo waya zaku yi ta kokawa.

Sai Musa Dan malam daga Kano, ya bugo waya, ya ce ya na yi wa manyan baki barka da zuwa da fatan alkairi

Sai wani mai gabatar da shiri ya ce a nan wannan layin wayar muna da kiran da ba a dauka ba kusan 300.

Sai Abdullahi Nalado yakujiba kunya, ina yi wa shugaban kungiyar Dillalan mai barka da fatan Allah ya dawo da shi gida lafiya, Allah ya kara daukaka shi bisa kokarin da yake yi na ganin harkar mai ya yi kyau a Najeriya baki daya.

Kabiru Mai biro yan dadi, daga Kano, sai layinsa ya katse.

 Kasan kanawa na son su ji su a waya”.

Injiniya Kailani ya ci gaba da yin kira ga yan Najeriya inda ya ce dole sai sun gyara kansu ya gyara halinsa domin wani akasi da aka samu na wannan batun mai da aka samu, sai NNPC ta fito da mai lita miliyan dari, amma zaka ga wani ya shiga layin mai idan ya sha man sai ka ga ya ta fi gida ya je ya zuke man don kawai a sayar da bayan gida a bakar kasuwa kuma duk gidan man da ka gani ana sayar da mai zaka ga yara da manya rike da jarkoki suna Sayarwa ta bayan fage ta yaya zamu ci gaba ana yin haka.

Kuma ana saran za a samu sauki nan gaba kadan

Injiniya dan dakata a yanzu an zo bangaren mu, inji shugaban Dillalan mai ya batun maganar tallafin mai da wani ya tambaya ko Injiniya bai fahimci tambayar ba ne.

Sai Injiniya kailani ya ce ai ya bayar da amsa kuma na ce NNPC ta cire hannunta amma idan ana son tallafin mai ya ci gaba a koma majalisar dokoki ta kasa, amma za a ci gaba da shi na tsawon shekara daya nan gaba.

Shugaban Dillalan mai to, mai tambaya ba zai  ba zai ga ne cewa gaskiya ba ne sai ya je ya sayi bakin mai zai tantance abin da ake nufi da hakan zai kuma ga ne.

Idan mutum na son yin bincike sai ya shiga yanar Gizo ya shiga cikin kasuwar duniya ya ga shin nawa ake sayar da danyen man nan nawa ake sayar da shi, ko domin mu yan Najeriya ne kawai sai a rika yin abin da ake so NNPC ta dauki kudi kawai ta Sanya a cikin aljihunta to, ba haka ba ne.

 Amma mutum yaje ya sayi bakin mai ko Kananzir sai ya ga ne da tallafi ko babu.

 Kuma a maganar da Injiniya ya yi da a kwai harin da ya dace in kai masa amma duk na share.

Injiniya Kailani ya ce jama’a maganar da ya yi na yi bayani a kan tallafi kuma sai wanda bai ga ne ba kawai har Gobe Gwamnati na bayar da tallafi a kan 145 zuwa 155 da ake Sayarwa kaga tallafin nan ya na nan abin da nake nufi kenan.

Kaga idan Gwamnati ta shigo da wannan man akwai masu wuraren ajiyar mai na kashin kansu ana ba su farashin 130 mu kuma a yau abin da NNPC ke sayar da mansu shi ne 148.17.

Kusan kowace litar mai na kanawa Gwamnati kan kudi naira 400 man ke zuwa Najeriya amma ita Gwamnatin na sayar wa 130 don haka nauyin da Gwamnati take dauka a kan wannan ba karamin abu ba ne mutane ya dace su Sani saboda haka ayi adalci ga Gwamnati kan kokarin da take yi.

Ina zuwa don Allah zan yi gyara Inji Dokta Injiniya Kailani, sai ta kacame a tsakanin dan Malam da kuma Injiniya Kailani sai dai masu gabatar da shirin sun ce akwai fa jama’a kan layi.

Fatima mai kamis,daga Kaduna hayin Kogi, ta bugo waya, ta ce ita ta na son ne a yi mata bayani a game da man da aka shigo da shi aka samu matsala.

Duk da irin matakan da ake da su a kan iyakoki ko ina amma a shigo da wani mai can da ban mai matsala, shin yaya za su yi da Injunan mutanen da suka samu matsala? Za a rage masu asarar da suka yi ne?

Ya na da kyau Malam Fatima, inji shugaban Dillalan mai ya ce hakika Gwamnati ta tashi tsaye ta hanyar hukumar NNPC domin ta hana a ci gaba da sayar wa da jama’a man da aka ajiye a wuraren ajiyar mai da ke da wannan matsalar kuma wadanda suka dauki man duk an ce masu su tsaya haka nan har sai an tantance tukunna.

Koda sun ta fi zuwa wuraren ajiyar mai ne na wadansu wuraren da ke Jihohi har sai an tantance tukunna, an kum a ajiye littafi a wuraren domin daukar alkalumma sosai domin duk wanda ke da magana nan gaba za ne me shi.

Na biyu kuma akwai wuraren da su suka dauki asara wato (dillalan mai) domin ana mayarwa da wasu kudinsu idan an samu matsalar a gidajen mai kuma nan gaba in an tantance duk za a warware komai.

Shaifullahi Kubarachi hayin kwari Madobi,karamar hukumar Madobi Jihar Kano ya bugo waya inda ya yi fatan alkairi da jinjina bisa yadda aka samu wayarwa da jama’a kai

Yanzu dai inji yan gidan rediyo masu gabatar da shirin suka ce ga Alhaji Bashir da Dokta Kailani.

Abubakar Musa Nuhu, ina yi maku fatan alkairi game da wayar da kan jama’a da fatan Allah ya yi riko da hannayenku.

Shin wai harkar mai ya zama masu gidajen mai su ne masu laifi domin sai inji kowa in ya tashi Dora laifinsa a kan masu mai ne kawai

Shin meye matsalar kuma me ke faruwa ne kuma sau da yawa sai inji su kansu kuka suke da abubuwan shin yaya abin yake ne kowa harkar mai harkar mai kawai.

Gwamnati ta yi abin da ya dace mana yadda mutane za su waraka sosai da fatan Allah ua mayar da baki gida lafiya.

Bashir Dan Malam, abin da ke faruwa a da can baya shi ne jami’an Gwamnati da yan barandan Gwannati da yan kusa da Gwamnati sai su shigo kafafen yada labarai sai su fadi abin da suke so a da can misali gidajen rediyon mu a da zaka gansu ba su da yawa sannan an shiga rediyon Kaduna ko na Jihar Kaduna duk na Gwamnati ne sai mutum ya fadi abin da bai kamata ya fadi ba wani ya ce mota dari ta taho Kaduna ko mota miliyan kaza aka bayar, amma a yanzu akwai gidajen rediyoyi da yawa da mutum ya fito zamu yi masa martani kawai.

Sai jami’an Gwamnati da yan barandan Gwamnati suka Dora mutane cewa mai gidan mai ke cutarwa, amma kuma idan yau Gwamnatin kaduna na son harkar ruwa ta yi tsada ta san yadda za ta yi domin da ta rike kayan shikenan, haka kuma idan tana son ya yi arha sai ta sako shi kawai.

Saboda haka wannan zargin da ake yi mana a da can ba mu da gata ne amma a yanzu ba haka ba ne, domin ko jami’in Gwannati ko mai fashin baki ana ganinsa mai daraja sai ya fadi abin da kawai ya ga dai dai ne.

Amma yanzu duk wanda ya fito kana fitowa Nima sai inje na masu zaman kansu in yi wannan domin al’amura duk sun waye akwai kalubale.

Akwai wanda ya ce ya na tambaya shin ana ganin man nan ya kusa karewa da Ibrahim Alaramma ya yi .

Injiniya Kailani ya ce to, wannan Gwamnatin na da shiri sosai na motocin da suke amfani da tsarin Gas saboda Iskar Gas da ke Najeriya ya fi man fetur yawa.

Ai gas ya fi gurbataccen danyen mai tsada saboda haka hukumar NNPC ta saka maganar batun Iskar Gas a gab, wani dan tsaiko aka samu amma da yanzu an ce za a Gwada amma an samu dan tsaiko da can daga kasashen kudi za su fara amfani da shi

Ai maganar karewar man fetur na Neja Dalta ne ake cewa zai kare amma a yanzu ake samun mai a ko ina domin a yanzu ba gashi a Arewa ba a wurare da yawa.

Amma Amurka da Turai abin da suke magana shi ne man nan ya ishesu shi yasa suke son a koma batun amfani da Iskar Gas kuma ana nan ana yin kokari ba da dadewa ba za a fara yin amfani da shi, kuma ni ba na zo nan in yo musu bane sai yazo ya kushe ni kuma ya na da wata magana ni cikakken bayanin da na yi .

Kafin ka sauka wannan man da ake magana an kawo gurbataccen man Jirgin sama ne shin me zaka ce?

Injiniya Kailani, domin na ga wani dan majalisa ya yi wannan bayanin cewa inda man jirgin sama ne da zai zama da hadari kwarai domin za a yi Gobara kwarai mutane za su mutu, amma ai ba na Jirgin saman ba ne.

Kamar bayanin da na yi tun da farko man da ya shigo an kuma tabbatar da yawansa da duk abin da ya dace har an amince da shi wanda duk kamfanonin da ake da su guda hudu da masu aikin duba wa duk sun tabbatar da cewa man bashi da wata matsala ko kadan.

Kuma ya dace yan jarida su yi binciken wai su waye suka yi wannan aikin har aka samu matsalar wannan sinadarin da ke gurbata mai

Injiniya Kailani, wato shi abin da kawai yake fadi a kan Dillalai ne masu zaman kansu amma ni nawa ina fadin komai ne baki daya.

Bashir Dan Malam ya ce shi a yadda ya fuskanci wannan al’amari shi ne ba da gangan aka yi ba.

Sai Gwamnati ta tashi tsaye kada lamarin ya faru a kan man Jirgin sama kawai shi ne bayani.

Injiniya Kailani, indai akwai ire iren su Bashir to sai su rika wasu bayanai kawai domin bayan an ce mai lafiya yake aka kuma ce gashi yanzu an samu wannan sinadarin a cikin man fetur saboda me

Masu gabatar da shirin rediyon suka ce akwai sakonnin da suka samu guda Saba’in da Tara (79) to dan debo wasu kuma mafi yawa sun yi magana a kan kungiyar Dillalan mai ne, akwai

Alhaji Mai kudi daga Afafa Legas ya ce wai wa zai dauki nauyin motocin da suka lalace yanzu ku zaku biya su ko Gwamnati ko waye?

Sai Kuma Sada Rabe daga Kafur, ya ce me yasa mutanenku ke bude gidajen mai da daddare saboda a yankin mu gaskiya ana yin haka nan akwai

Auwalu saga Jihar Nasarawa, ko an cire tallafin mai domin ya ce su a yankinsu suna sayen mai a kan naira 200 ne

Wani ya ce wai meye wannan tallafin yake da shi ne

Wani daga Gombe ya ce me ya sa ake samun bambancin farashi a gidajen mai

Adam Yusuf Gwaska saga Jos ya ce shin wai me ya sa ku Dillalan mai na zaku zo ku kafa matatun mai ba

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.