Daga Imrana Abdullahi
Babban Bankin Najeriya ya bayyana cewa su a koda yaushe suna yin biyayya ne ga umarnin da shugaba Muhammadu Buhari ya bayar na yin amfani da tsohuwar takardar naira dari biyu (200) kawai.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun mataimakin Gwamnan babban Bankin Edward L Adamu da kuma Darakta mai kula da harkokin yada labarai Mista Osita Nwanisobi.
Takardar ta ci gaba da bayanin cewa Babban Bankin ya ce an jawo hankalinsa a game da wata takarda mai dauke da bayanan karya da ba su da tushe balantana makama.
Bayanan wai cewa shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin cewa Babban Bankin ya ci gaba da bayar da takardun kudi na naira dari 500 da naira dubu 1000 da nufin a ci gaba da kashe su a cikin kasa, hakika ba gaskiya bane.
Babban Bankin Najeriya ya tabbatar da cewa “su a koda yaushe suna nan a kan irin umarnin da shugaban kasa ya ba su, na yin amfani da tsohuwar takardar naira dari biyu 200 kuma za a rika yin amfani da ita a cikin al’umma domin amfanin yau da kullum”.
A saboda haka ne suke yin kira ga daukacin jama’a da su dawo daga Rakiyar bayanan karyar da ake yadawa domin ba su da kamshin gaskiya.
Takardar ta ci gaba da bayanin cewa “Bankin na yin aiki tare da sauran hukumomin tsaro da nufin yin bincike, a kama tare da yi wa wadanda suka yada bayanan karyar hukuncin da ya dace da su ko. Don haka ya dace a yi hattara.