Home / Labarai / BABBAN HAFSAN TSARON NAJERIYA  CHRISTOPHER MUSA YA ZIYARCI JAGORORIN MAJALISAR KOLI NA MUSULUNCI A MASALLACIN TSAKIYA NA ABUJA

BABBAN HAFSAN TSARON NAJERIYA  CHRISTOPHER MUSA YA ZIYARCI JAGORORIN MAJALISAR KOLI NA MUSULUNCI A MASALLACIN TSAKIYA NA ABUJA

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna

Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa, ya kai ziyarar tabbatar da zaman lafiya ga shugabannin majalisar koli ta harkokin addinin musulunci a masallacin kasa da ke babban birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a.

Babban hafsan sojan ya bayyana cewa, makasudin ziyarar tasa ita ce karfafa alaka tsakanin sojojin Najeriya da malaman addini a duk fadin kasar.

Babban Hafsan ya bayyana cewa Sojoji na ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da kabila ko addini ba.

Ya kara da cewa sojoji ba su da alaka da siyasa kuma za su yi duk mai yiwuwa don kare martabar yankunan kasar daga wuce gona da iri.

Ya yi kira ga malaman addini a Najeriya da su yi amfani da wannan matsayi da aka ba su wajen samar da zaman lafiya da hadin kan da ake bukata domin ci gaban tattalin arzikin kasa.

Ya kuma bayyana cewa da zaman lafiya ne kadai za a iya samun ci gaban kowace irin kasa a fadin duniya.

Babban Limamin Masallacin tsakiyar da ke Abuja Sheikh Farfesa Ibrahim Ahmad Maqari da sauran Limamai da suka halarci taron sun gode wa hafsan sojin bisa wannan ziyarar, inda suka ce dukkan limaman masallacin tsakiya da sauran masallatai da ke babban birnin tarayya su ne masu kawo zaman lafiya a cikin wa’azin da suke yi. duk abin da suke yi.  Saboda haka Mambobin Majalisar sun tabbatar wa babban Hafsan tsaron na Najeriya cewa za su ci gaba da yi wa kasar nan addu’ar zaman lafiya.

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.