Home / Kasashen Waje / Juyin Mulki A Nijar A Tuntubi Masana Huldar Kasa Da Kasa – Sadiq Abubakar

Juyin Mulki A Nijar A Tuntubi Masana Huldar Kasa Da Kasa – Sadiq Abubakar

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna

 

 

Wani masanin yin hulda da kasashen waje kuma Malamin jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya Dokta Sadiq Abubakar ya yi kira ga shugabanci da yayan kungiyar ECOWAS da su bi ahankali domin irin yadda kungiyar ta bayar da lokaci da kuma umarni ga sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Nijar cewa ba dai- dai bane kuma an yi saurin yin hakan.

 

Dokta Sadiq Abubakar ya yi wannan kiran ne jim kadan bayan kammala gabatar da wata lacca a kan batutuwan juyin mulkin kasar Nijar da kwamitin Da’awa na masallacin ITN Zariya suka shirya.

 

 

Ya ce “hakika an yi sauri a kan irin matakin da kungiyar ECOWAS ta dauka ga yan juyin mulkin kasar Nijar inda ya ce ba a yin haka, har sai an tabbatar da cewa za a iya daukar matakin hukunci ko aiwatar da matakin da za a dauka kafin a bayyana matakin.

 

 

Dokta Sadiq ya ci gaba da bayanin cewa ya dace a yi tuntuba ga ofishin Jakadancin Najeriya na kasar Nijar da kuma hukumar Leken asiri ta Najeriya (NIA) da kuma ma’aikatar harkokin kasashen waje ta Najeriya da an samu sahihan bayanai da ake bukata a Sani a game da duk batun yan juyin mulkin da aka yi a kasar Nijar, amma irin matakin da aka dauka lallai ba a yin hakan”.

 

 

Ya kara da cewa kafin daukar matakinirin wanda kungiyar ECOWAS ta dauka sai mutum na da karfin ikon duk abin da ya ce ayi za a yi, wato mutum ya na da karfi kenan da zaka ce ayi kuma ayi kafin daukar matakin da aka dauka, kuma idan ba a yi ba ga matakin da zaka dauka sannan wanda ka ba umarnin ya san zaka iya daukar matakin da ka ce lallai zaka dauke shi, saboda haka babu wani dalilin yin yaki don haka sai ayi taron tattaunawa tsakanin bangarorin da ke hamayya da Juna a kasar ta Nijar da kuma kungiyar ECOWAS a zauna a teburin tattaunawa da Juna.

 

 

Kuma ya dace a Sani cewa akwai matsalar da ka iya faruwa ta wasu ma daga wadansu wurare a cikin duniya su shiga cikin lamarin da wata hanyar da ba a yi tsammani ba don haka muke cewa aje a zauna a tattauna da nufin a samu mafita a kan lamarin.

 

 

Dokta Sadiq Abubakar ya kuma yi kira ga shugabannin kungiyar ECOWAS da su daina daukar mataki har sai sun tuntubi masana tukunna a kan harkokin kasashen waje da a kullum suke aiwatar da aiki kamar yadda ya dace”.

 

 

“Kafin daukar mataki a kan dangantakar kasa da kasa su tuntubi kwararru wadanda ke a jami’o’I daban daban ban da kuma hukumar NIA da ma’aikatar harkokin kasashen waje da akwai dimbin masana da yawa da idan an tuntube su za su taimaka kwarai wajen daukar matakan da suka dace, koda yake a halin yanzu na ji an ce an canza lamarin kuma sun ce a dauki matakin tattaunawa

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.