Home / Big News / BABBAN SAKATAREN HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA JIHAR BAUCHI YA GANA DA MA’AIKATANSA.

BABBAN SAKATAREN HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA JIHAR BAUCHI YA GANA DA MA’AIKATANSA.

Jamilu Barau Bauchi

A yau Alhamis 4 ga watan Nuwamban shekara ta 2021,Babban Sakataren hukumar jin dadin Alhazai na jihar Bauchi Imam Abdul-Rahaman Ibrahim Idris ya jagoranci wata ganawa ta musamman da shuwagannin gudanarwa da sauran daukacin ma’aikatan hukumar,tare da yin kira gare su da su ci gaba da  sadaukar da kansu wajen gudanar da aiki tukuru.

A yayin gudanarda da zaman Babban Sakataren,Imam Abdul-Rahaman Ibrahim Idris yace ganawar wani bangare ne na himmatuwarsa wajen tabbatarda dabbaka manufofi da tsare-tsare domin cimma muradunsa.

Ya kuma bayyana bukatar dake akwai na neman goyon bayan al’uma da ma’aikatansa,inda yace sa hanun al’uma zai bada damar gudanarda aikin Hajji cikin nasara.

Imam Abdul-Rahaman ya kuma bukace su day suyi aiki tukuru wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

 

Sai ya karanto aya ta 2 sura ta 67 daga cikin Littafin Al-qur’ani mai girma dake cewa “Allah Madaukakin Sarki shine wanda ya halicci rayuwa da mutuwa yakuma jarabceku Dan yaga wadanda suka kyautata ayyukansu kuma shine mai girma kuma mai gafara”

Ya kara da cewa hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Bauchi za ta yi Shirin horasda ma’aikatanta ta hanyar da ta dace domin basu damar gudanarda ayyukansu yanda ya kamata.

Shima da yake nasa yawabin a gurin taron Daraktan Mulki na hukumar Malam Alkasim Danlami Shall ya yabawa sabon babban Sakataren bisa shirya taron ganawar a dai-dai wannan lokaci,tare da bayyana hakan a matsayin hanya mafi dacewa wajen cimma nasarorinda aka sanya a gaba.

 

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.