Home / Labarai / Babu inda na ce nafi Yan Najeriya Shan Wahalar Tsadar Rayuwa, amma ina Fatan Matsalar ta zamo Tarihi -Dangote

Babu inda na ce nafi Yan Najeriya Shan Wahalar Tsadar Rayuwa, amma ina Fatan Matsalar ta zamo Tarihi -Dangote

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa ya fi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.
Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .
Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote ya yi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.
“Duk abin da ya shafi yan Najeriya ya shafemu”, inji Sanarwar.
Dangote ya Kara da cewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun  da ba su samu damar biya ba a baya.”
Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A  bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari,  gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.
“Muma muna siyan muhimman kayan abinci a kasuwa kamar yarda kowa ke saye don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen  ciyar da al’umma.” Dangote.
Shugaban kamfanin ya yi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda ya ce shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda ya yi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.
“Kamfaninmu ya kasance mai bin dokokin kasa a koda yaushe tare da  neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”
Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada  rade-radi da jita-jita haka kawai.

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.