Home / Labarai / BABU KAMSHIN GASKIYA A LABARIN MAIDO DA CIN HANCIN WASU KUDADE DAGA MAMBOBIN PDP.

BABU KAMSHIN GASKIYA A LABARIN MAIDO DA CIN HANCIN WASU KUDADE DAGA MAMBOBIN PDP.

 

Kwamitin zartaswa na jam’iyar PDP ya samu rahoto akan wasu labaran kanzon kurege dake yawo a kafafen sada zumunta domin ɓata suna, akan wasu kudade da aka ce an bayar da su a matsayin alawus alawus na gidaje da aka baiwa wasu mambobin PDP da kwamitin zartaswar ta da kuma wau ma’aikata.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata Sanarwa da ke dauke da sa hannun Honarabul Debo Ologunagba Sakataren Yada labarai na kasa na jam’iyyar PDP da aka rabawa manema labarai.

 

A saboda haka, muna sanar da jama’a cewa wannan labari ne da bashida tushe balle makama, wanda wasu kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta suka dinga yadawa, inda aka ce alawus din gidajen na miliyoyin Naira an baiwa wasu mambobin jam’iyar a matsayin toshiyar baki ne.

To! muna so a sani cewa jam’iyar PDP bata samu wani sakon maido da kudi a asusun ta ba, da sunan wani ne daga cikin mambobin NWC.

Abinda yake na hakikanin gaskiya shine, kudaden da aka ce an fitar na alawus din hayar gidaje, an bayar da su ne ta hanyar da ta kamata bayan cika dukkanin kaidoji kamar yadda dokokin jam’iyar PDP suka shata ga dukkanin ma’aikatan dake karkashin ta.

A saboda haka idan har wani yayi tunanin ya maido da kuɗin da aka bayar a kashin kansa, to babu yadda za a yi a bayyana su a matsayin cin hanci, domin an fitar da kuɗin a kan ka’ida ne.

A karshe, jam’iyar PDP na kira ga dukkanin mambobin ta da magoya baya da su yi watsi da wadannan  labarai na kanzon kurege da aka ƙirƙira domin bata sunan wannan jam’iya, ko kuma yunkurin kawar da hankalin al’umma daga manufofin mu, domin ganin an ceto ‘yan Najeriya daga ƙangin da suke ciki na mulkin APC.

 

 

 

 

About andiya

Check Also

An Zargi PDP Da Ayyukan Ta’addanci A Jihar Zamfara

Gamayyar Kungiyoyin Kwararru Na Dattawan Arewa Sun Kalubalanci Kalaman PDP A Game Da Batun Tsaron …

Leave a Reply

Your email address will not be published.