Related Articles
IMRANA ABDULLAHI
Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa babu wani bangare da ya samu matsala a dukkan ma’aikatu da sauran bangarorin Gwamnati sakamakon shigarsa harkokin siyasa a matakin kasa.
Aminu Waziri Tambiwal, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da kafar yada labaran Talbijin ta trust.
Gwamna Tambuwal ya ci gaba da cewa “al’ummar Jihar Sakkwato sun san mutumin da suka zaba tun daga lokacin da aka zabe ni a majalisa na zama mutum na hudu a matakin Gwamnati a tarayyar Najeriya inda na zama shugaban majalisar wakilai ya zuwa yanzu da na zama Gwamnan Jihar Sakkwato, don haka jama’ar Jihar Sakkwato sun Sanni shi yasa a koda yaushe suke ba ni amana”.
Ya kara da cewa “a halin yanzu yadda duniya ke tafiya da zamani mutum zai iya tafiyar da aikin Gwamnati daga ko’ina, don haka ina bayar da tabbacin cewa ba wani bangaren da ke da wata matsala sakamakon kokarin da nake yi a harkokin siyasa na kasa baki daya”, inji A Tambuwal.