Home / Garkuwa / Bafarawa Ya Kusa Kammala Jami’ar Karatun Kur’ani A Shinkafi

Bafarawa Ya Kusa Kammala Jami’ar Karatun Kur’ani A Shinkafi

Bafarawa Ya Kusa Kammala Jami’ar Karatun Kur’ani A Shinkafi
Mustapha Imrana Abdullahi
Bayanan da wakilinmu ya samu daga wani babban hadimin tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa na cewa kadan ya rage slamic University for Qur’anic Studies a kammala ginin jami’ar karatun Alkur’ani da ke garin Shinkafi a Jihar Zamfara.
Majiyar mu ta tabbatar mana cewa tsohon Gwamnan Sakkwato Attahiru Dalhatu Bafarawa (Garkuwan Sakkwato)  tare da Shaikh Abdullahi Bala Lau, shaikh Kaboru Gombe da sauran wadansu manyan malamai suka halarci inda ake ginin wannan katafariyar jami’a domin karanta Kur’ani mai tsatki a garin Shinkafi cikin Jihar Zamfara.
Shi dai ginin wannan jami’ar tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato ne da kansa yake kashe dukiyar da Allah ya bashi yana gina wannan jami’a domin ciyar da musulunci gaba a duk fadin kasa baki daya.

About andiya

Check Also

Ramadan 2023: Nigerian Church Reaches Out To Over 1000 Underprivileged Muslims/ Almajiri.

  The church of Christ Evangelical and life Intercessory Ministry, Sabon Tasha Kaduna State has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.