Home / Labarai / Jihar Kano Ta Rufe Gidajen Kallo, Wuraren Taro

Jihar Kano Ta Rufe Gidajen Kallo, Wuraren Taro

Jihar Kano Ta Rufe Gidajen Kallo, Wuraren Taro
 Imrana Abdullahi

 

A kokarin ganin an dakile yaduwar Cutar Korona a Jihar Kano Gwamnatin Jihar karkashin Gwamna Ganduje ta bayar da umarnin ma’aikatan Gwamnati su zauna a Gida.
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da rufe gidajen Kallo da kuma wuraren yin taron jama’a duk a kokarinta na yaki da yaduwar cutar Korona.
Kwamishinan yada labarai na Jihar Kano Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ya Sanya wa hannu da aka rabawa manema labarai
Kwamishina Muhammad Garba ya ce Gwamnatin ta dauki wannan matakin ne domin dakile yaduwar cutar Korona a dukkan fadin Jihar baki daya.
Kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba, ya ci gaba da bayanin cewa an dauki wannan matakin ne a wajen taron masu ruwa da tsaki da aka yi a gidan Afrika cikin gudan Gwamnati da ke Kano a ranar Litinin.
Ya kara da cewa an umarci dukkan ma’aikata da su zauna a gida har sai an bayar da sanarwar umarni na gaba.
Malam Garba, sai dai ya bayyana cewa ma’aikatan da suke aiki na musamman kamar ma’aikatan lafiya,masu aikin kashe Gobara, ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha,
Masu koyarwa, Jami’an tsaro da kuma yan jarida duk ba su a cikin wannan matakin da Gwamnati ta dauka.
Kwamishinan ya kara jaddada kudirin Gwamnatin Jihar Kano na yin aiki da masu ruwa da tsaki da suka hada da Malamai domin tabbatar da mutane na bin ka’idoji da tanaje tanajen yaki da cutar Korona.
Ya kuma yi gargadi ga jami’an tsaro da yake suna cikin masu ruwa da tsaki a harkar da kada su yi sako sako ga duk wanda ya kasa yin biyayya ga wannan matakin Gwamnati.

About andiya

Check Also

Majalisar Wakilai: Sani Jaji Zai Maye Gurbin Abbas Tajuddeen?

Daga Imrana Abdullahi Kamar yadda wadansu bayanai suka bayyana a kafar yada labarai ta jaridar …

Leave a Reply

Your email address will not be published.