Home / Labarai / Bam A Tudun Biri: A Biya Diyya Ga Wadanda Suka Rasa Rai – Aliyu Waziri San turakin Tudun wada

Bam A Tudun Biri: A Biya Diyya Ga Wadanda Suka Rasa Rai – Aliyu Waziri San turakin Tudun wada

 

Daga Imrana Abdullahi
Shugaban majalisar kolin Kungiyar masu Noman Zamani Alhaji Dokta Aliyu Muhammad Waziri, San turakin Tudun wada Kaduna, Kadimul Islam ya yi Kira ga Gwamnatin tarayyar Najeriya da ta biya diyyar ran wadanda suka mutu da kuma daukar nauyin wadanda suka samu rauni ko jikkata a sakamakon harin Bam din da aka kai wa masu Maulidin annabi a  kauyen tudun biri da ke karamar hukumar Igabi a Jihar Kaduna.
Santurakin Tudun wada Kaduna, da ake yi wa lakabi da Dan marayan Zaki, Alhaji Dokta Aliyu Muhammad Waziri ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya kira a garin Kaduna.
Aliyu Waziri ya ci gaba da cewa hakika akwai bukatar biyan diyyar rayukan da aka rasa a sakamakon harin Bam din da aka kai a kauyen Tudun Biri lokacin da mutanen na gabatar da bikin Maulidin fiyayyen halitta Annabi Muhammadu ( S.A.W)
Kuma kamar yadda rundunar soja ta tabbatar cewa kuskure ne don haka lallai a biya niyya kuma a dauki nauyin maganin wadanda suka ji rauni a sakamakon harin bam din.
Aliyu Waziri ya kuma jinjinawa shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu bisa irin kyawawan tsare tsaren da yake yi wa aikin Noma da kuma gabatar da tsarin samar da kasa da abinci da nufin samun abubuwan da ya dace a kasa har ma da kasashen Ketare.
“Muna kuma yin kira da babbar murya ga Gwamnatin tarayya da ta gudanar da bincike game da wannan lamari na harin bam da aka yi a kauyen Tudun biri da ke karamar hukumar Igabi”.
Sai dai ya kuma yi addu’ar Allah ya tona asirin duk wadanda ke haifar da fitinar da za ta haifar da tashin tashina a duk fadin Najeriya.

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.