Mustapha Imrana Abdullahi
Wani Malamin addinin musulunci a tarayyar Najeriya mai suna Dokta Nura Khalid, ya bayyana rashin samun hadin kai a tsakanin malaman addinin Islama a matsayin babbar matsalar da ke addabar harkar Koyar da addinin musulunci a kasar.
Nura Khalid ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wa’azi a cikin shirin Wa’azin Juma’a da kafar yada labarai ta DITV da rediyon Alheri da ke Kaduna.
Inda ya bayar da misali da marigayi Shaikh Abubakar Mahmud Gumi da ya ce ya samu nasara ne sakamakon irin Akidar da ya dauka ta malaman farko wanda hakan yasa ya samu cikakkiyar nasara musamman a yankin arewacin kasar.
Sai dai Malamin ya bayar da misali irin rayuwar da malamai suke yi ta fuskar tafiyar da rayuwa irin ta Gwamnoni, wanda ya saba da koyarwar malaman farko
“Ka san Gwamnoni suna tafiyar da rayuwa ne domin duniya, amma malamai sai ka ga suma su na yin irin wannan rayuwar, sai kaga malami na son hawa mota da rayuwa irin ta Gwamna wanda hakan ya saba wa tsarin malanta tun farko”, inji shi.