Home / News / Hukumar Zaben Kaduna Ta Dage Zaben Kananan Hukumomi Hudu

Hukumar Zaben Kaduna Ta Dage Zaben Kananan Hukumomi Hudu

Mustapha Imrana Abdullahi

Hukumar zabe mai zaman kanta a Jihar Kaduna (KADSIECOM) ta sanar da dage zaben kananan hukumomi guda hudu a Jihar.

Shugabar hukumar Dokta Saratu Binta Dikko – Audu, ta bayyana hakan a wajen wani taron manema labarai a ofishin hukumar da ke Kaduna, a ranar Juma’a 3 ga watan Satumba 2021.

“An tabbatar mana da cewa a cikin Jihar nan da akwai rahoton batun matsalar tsaro don haka ba za a samu damar yin zabe a wasu kananan hukumomi ba”, inji Saratu Dikko Audu.

Saboda haka domin a kare rayuwa da dukiyoyin mutane da suka hada da masu zabe da kayan zaben don haka dole sai mun Dakatar da zaben a wasu kananan hukumomi sai nan gaba za a sanar da ranar da za a yi zabe a nan gaba

“Don haka hukumar zabe mai zaman kanta ke sanar da Dakatar da yin zabe a wadannan kananan hukumomin da suka hada da 1- Birnin Gwari 2- Chikun 3- Kajuru 4 – Zangon Kataf”, inji Saratu.

Za a tabbatar da an kai wadatattun jami’an tsaro a wadannan kananan hukumomi domin kare lafiya da dukiyar jama’a “, inji ta.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Kaduna ta kuma sanar da ranar 25 ga watan Satumba 2021 a matsayin ranar da za a yi zabe a wadannan kananan hukumomi hudu da aka sage zabensu.

 

About andiya

Check Also

PDP National Chairman morns Tambuwal Advisor

  Dr Iyorchia Ayu, the National Chairman of Peoples Democratic Party (PDP), has commiserated with …

Leave a Reply

Your email address will not be published.