…Kuma Bana goyon bayan yin Yan Sandan Jihohi
Bashir Bello, Daga majalisar Abuja A Najeriya
Shugaban Kwamitin Gyaran Titunan Gwamnatin taraiya na Majalisar Dattawa Sanata Babangida Hussain, ya shaidawa manema labarai cewa bai Gamsu da irin yadda ake kafa jami’an da ake kira da yan sa kai ba, domin horon da ake ba su bai wadatar ba.
Sanata Hussaini ya nuna rashin goyon bayansa na yadda ake kafa Yan Sakai, inda ya ce horo da ake ba su, bai wadata ba domin mafi karanci horo da ya kamata a ba su shi ne na shekara guda kuma kamata ya yi ayi amfani da su wajen samar da bayanai ga jami’an tsaro ba a ba su bindiga ba saboda yin hakan yna da na tasa illar.
A daya bangaren ma ya nuna rashin goyon bayansa na yunkurin da wasu ke yi na kafa Yan sandan Jihohi in da ya ce har yanzu Siyasarmu Jaririya ce lura da yadda muke gudanar da ita.
“Akwai yiwuwar yin amfani da Su wajen cizgunawa abokan adawa da kuma yin abubuwa da basu kamata ba.
Sai dai “Sanatan wanda ya ce abu mafi mahimmanci wanda yake ganin zai magance matsalar kasarnan ita ce saka kishin Kasa a zuciyar duk yan Najeriya tun daga Firamare wanda idan akwai Kishin Kasa wasu abubuwan ma ba za a aikatasu ba saboda kishi”, inji Sanata Babangida.
Saboda haka ne Sanatan ya yi Dogon jawabi a kan irin bukatar da ake da ita domin wayar da kan Yan Najeriya a game da batun Kishin Kasa a tsakanin al’umma baki daya.
Sanata Babangida ya kuma bayar da misali da irin yadda lamarin yake lokacin suna yara yadda tun daga makarantar Firamare ake raba masu tutur Najeriya musamman wajen bikin ranar samun Yancin Kai da sauran su.
Har ila yau, ya ce a kasashe irin su Amurka ma za ka ga kowanne kofar gida akwai tutar kasar da kuma fito da tsare-tsare da za su saka kishin kasa a zuciyar jama’ar kasa baki daya.