Home / Big News / Bana Jin Tsoron Kowa Sai Allah – Aminu Waziri Tambuwal

Bana Jin Tsoron Kowa Sai Allah – Aminu Waziri Tambuwal

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Barista kuma Honarabul Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa a matsayinsa baya jin tsoron kowa sai Allah kuma kowane irin mahaluki ne shi kowane ne shi.
“Bani da wani abu da na yi da nake gudun a dauko shi ayi Mani Gurudau, ya ce ka san Gurudau,babu shi sai dai ko sharri na siyasa kawai azo ace na sace biliyan dari da Goma sha Bakwai nan Sakkwato ke cewa ko, to ba na jin tsoron kowa sai Allah.
Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da kafar yada labarai ta Gidan rediyon Jamus (DW)
A game da batun gayyatar da hukumar Efcc ta yi masa a kwanan baya sai ya ce bincike na ci gaba domin har yanzu ina zuwa Efcc ko a ranar 2 ga watan Afrilu yanje Efcc ban dena zuwa ba kuma kowane sati Uku sai naje Efcc har dai sai an kammala bincike za su bayyana abin da za su yi ko za su kai Kotu ne ko kuma ba kotun za su ba lallai za su yi bayani idan an kammala, mu mun san mulki na Allah ne kuma shike bayar da shi ga wanda yaga dama a sadda yaga dama.
In Allah ya yarda Duk taron su Allah zai zare abin (mulki) a hannunsu ya kawo sauki da nasiha ga rayuwar talakan Najeriya, zamu yi duk abin da zamu yi muga an fitar da dan takara daya kuma shima zaben fitar da dan takara ma ai Dimokuraɗiyya ce sai ayi zaben kuma daga bayan in an ma yi zaben sai a marawa dan takara daya baya

About andiya

Check Also

Dangote, Pope Leo XIV, Trump, Xi Jinping, others Named in TIME 100 Most Influential People for 2026

  Renowned African industrialist and philanthropist, Aliko Dangote, has been named among TIME Magazine’s 100 …

Leave a Reply

Your email address will not be published.