Related Articles
Bani Dauke Da Cutar Korona – El Rufa’I
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’I, ya bayyana cewa bashi dauke da wannan cuta ta Korona.
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da kafafen yada Labarai a cikin gidan Gwamnatin Jihar da aka yada kai tsaye.
Gwamnan ya ce daman ya killace kansa ne sakamakon aikin da ya yi da wadansu manyan jami’an Gwamnatinsa tun bayan da ya dawo daga tafiya.
“To wannan dalili ne yasa na killace kaina na wasu kwanaki, kasancewa an samu wadansu manyan jami’an Gwamnati da wasu a gidana suna dauke da wannan cuta da a yanzu suna nan suna shan magani”.
Gwamnan ya ci gaba da cewa daga yau zan ci gaba da kasancewa a wurin aiki kuma za a ganni ina aikace aikace kamar kowa tun da bani dauke da cutar.
Ya kara da cewa hakika wannan cutar ta dawo karo na biyu don haka kowa ya yi hattara a ci gaba da kiyayewa da doka da ka’idar dakile wannan cutar.
” A wannan lokaci da cutar ta dawo tuni har ta halaka wasu mutane cikinsu har da wadansu fitattu a kasa”.