Home / Labarai / Idan Aka Ki Bin Doka Zamu Koma Gidan Jiya – El – Rufa’I

Idan Aka Ki Bin Doka Zamu Koma Gidan Jiya – El – Rufa’I

Idan Aka Ki Bin Doka Zamu Koma Gidan Jiya – El – Rufa’I
Mustapha Imrana Abdullaho
Gwamnan Jihar Kaduna ya bayyana cewa idan aka ki bin dokar yin taro, cinkoso a wurare da kasuwanni, rashin bin doka a wurin sayar da abinci da sauran ka’idoji zamu koma gidan jiya na rufe Jihar Kaduna.
Gwamnan Jihar Kaduna ya ce daga Gobe za a rika tabbatar da bin doka ta hanyar kotun ta fi da gidanka domin hukunta duk wanda yaki Sanya Takunkumin rufe hanci da baki da sauran bin dokokin dakile yaduwar cutar Korona.
“Idan na fita da kaina ina lissafa mutane da nake gani amma sai kaga kalilan ne ke amfani da Takunkumin rufe baki da hanci wanda hakan ya sabawa ka’idar da aka tanadar.
Don haka idan aka ki bin dokokin dakile Korona to lallai za a koma yar gidan jiya, amma fa Gwamnati bata son rufe Jihar sai ya zama dole saboda muma muna samun kudin shiga daga kasuwancin da ake yi.
Gwamnan ya ci gaba da cewa kada mutum ya Sanya takunkuminsa a cikin aljihu domin ba mu son kowa ya rasa ransa, domin tun wanda ya rasa rai sai Allah ya tambaye mu ta yaya aka yi.

About andiya

Check Also

PRESIDENT TINUBU COMMENDS DANGOTE GROUP OVER NEW GANTRY PRICE OF DIESEL

  President Bola Tinubu commends the enterprising feat of Dangote Oil and Gas Limited in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.