Daga Imrana Abdullahi, Kaduna
Yunkurin da gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal keyi domin ceto jihar na kara samun ci gaba yayin da ya sake kulla yarjejeniya da bankin duniya domin zuba jari mai tsoka a jihar musamman a fannin ilimi, kiwon lafiya, rage radadin talauci da samar da ababen more rayuwa.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun Nuhu Salihu Anka, Darakta Janar na yada labarai da sadarwa, ofishin gwamnan zartaswa da aka rabawa manema labarai.
Bayanin hakan dai ya fito ne a lokacin da Gwamnan ya kai ziyarar ban girma ga bankin duniya a ofishinsa da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya
Gwamna Lawal wanda ya nemi babban bankin duniya ya shiga tsakani na musamman, ya ce jihar na fuskantar kalubale masu tsanani wanda ke bukatar tallafi daga kungiyoyin kasa da kasa kamar bankin duniya don taimakawa wajen rage radadin talauci, kawo karshen rashin tsaro, bunkasa harkar kiwon lafiya, ilimi, samar da ruwan sha, ababen more rayuwa da dai sauransu.
Ya kara da cewa Jihar Zamfara a matsayinta na mai fama da talauci tana sha’awar hada hannu da Bankin domin jihar ta lalace kwata-kwata, yana mai cewa gwamnatinsa ta dauki matakin rage kudaden da ba a bukatar a kashe haka kuma Gwamnatin ta rage yawan kudaden da ake kashewa.
Gwamnan ya kara jaddada rokonsa ga bankin duniya da ya baiwa jihar kulawa ta musamman kan ayyukan da take yi wa ‘yan Najeriya.
Daga nan sai ya nuna jin dadinsa da irin tarbar da ofishin bankin duniya na Abuja ya yi masa.
A nasa jawabin, daraktan bankin duniya a Najeriya, Shubham Chaudhuri wanda ya sake gabatar da ayyukan bankin ga gwamnan ya ce a shirye suke su hada kai da gwamnatin Jihar Zamfara, wajen bayar da tallafin kudi da sauran ayyuka.
Ya ba da tabbacin cewa bankin duniya zai zuba jari a shirye-shirye kamar rage radadin talauci, ingantaccen tsarin kiwon lafiya da samar da ababen more rayuwa a jihar a cikin hadin gwiwa mai karfi na ilimin yara mata, wanda bankin duniya ke taimakawa jihar, yana mai cewa za a inganta shi sosai.
Tare da bayyana cewa za su kuma taimaka wa jihar wajen habbaka samar da kudaden shiga domin samun ci gaba mai dorewa.
Gwamnan ya samu rakiyar sakataren gwamnatin jihar Alhaji Abubakar Nakwada; Shugaban Ma’aikata; Hon. Mukhtar Lugga, sakataren Gwamnan , Mannir Baba, da masu taimakawa Gwamnan a kan harkar bunkasa tattalin arziki Mu’azu Barau, Ibrahim Modibbo da ke kula da ayyukan musamman da sauran mataimakan Gwamnan a kan harkar yada labarai da dai sauransu.
13 ga Yuli, 2023