Home / Uncategorized / Bankin Keystone Ya Jinjinawa Kokarin Gwamna Lawwl Na Zamfara

Bankin Keystone Ya Jinjinawa Kokarin Gwamna Lawwl Na Zamfara

Bankin Keystone ya jinjina wa namijin ƙoƙarin Gwamna Lawal wajen samar da manyan abubuwan more rayuwa ga al’ummar Jihar Zamfara.
Manajan Daraktan Bankin, Hassan Imam ne ya jagoranci manyan jami’an gudanarwar bankin a ziyarar ban girma da suka kai wa gwamnan, ranar Asabar a gidan gwamnati da ke Gusau.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa bankin na gyaran makarantar firamare ta Sarkin Kudu da kuma makarantar sakandare ta Sambo, duk a babban birnin jihar, a matsayin wani ɓangare na kyautata wa al’ummar da ke kira ‘Corporate Social Responsibility’ (CSR).
Yayin da yake jawabi ga shugabannin bankin, Gwamna Lawal ya yaba da ƙoƙarin Keystone tare da jajircewarsu wajen ganin jihar Zamfara ta kasance cikin yanayi mai kyau ga kowane ɗan kasuwa.
“Sanin kowa ne cewa mun gaji tsarin da ba ya aiki sosai a jihar Zamfara. Duk da haka, wannan ba uzuri ba ne na kasa yin aiki yadda ya kamata. A maimakon haka, mun mai da hankali kan lalubo mafi kyawun hanyoyin ci gaban jihar, kuma abin da muka tsayu a kai kenan.
“Ilimi yana da matuƙar muhimmanci ga duk abin da muke yi a rayuwar mu. Ya zama ƙashin bayan kowace ingantacciyar al’umma. A gwamnatina ilimi shi ne abu na biyu bayan tsaro.
“Ina so in nuna godiyata da wannan karimcin. Kamar yadda na ambata, wannan aiki zai shiga cikin tarihi a matsayin shaida ga rawar da bankin ku ke takawa a tarihin nasararmu.
“In Sha Allahu, Zamfara za ta ƙara ƙaimi da jajirce wajen ganin mun yi gogayya da sauran jihohin Nijeriya ta kowane fanni.
“Ina fatan ƙaddamar da waɗannan makarantu nan ba da jimawa ba da kammala su. Na gode ƙwarai da wannan karamci.
Tun da farko, Manajan Daraktan Bankin Keystone, Hassan Imam, ya bayyana cewa, hukumar gudanarwar bankin ta tattauna ne kan batun shiga tsakani kafin yanke shawarar mayar da hankali kan sake gyarawa da kuma inganta makarantu gaba ɗaya a wani bangare na Kyautata Wa Al’umma.
“Nasarar da wannan gwamnati ta samu a cikin watanni 17 kacal ya zarce abin da magabatanta suka cimma a cikin sama da shekaru 20. Gwamnatin Dauda ta yi fice a fannin ilimi, lafiya, da ababen more rayuwa. Bani da isasshen lokacin da zan jera duk abin da ta yi wa jihar Zamfara, amma duk wanda ya ziyarci jihar zai shaida yadda aka yi aikin titi na biliyoyin daloli.
“Mun zo nan ne domin mu ba ku goyon baya, saboda mun fahimci kwazon da ku ke yi, bayan tattaunawa da dama, mun yanke shawarar mayar da hankali kan ilimi, sannan muka zabi makarantun firamare da sakandare guda biyu. Muna gudanar da cikakken gyare-gyare a Makarantar Firamare ta Sarkin Kudu da Makarantar Sakandare ta Sambo, da ke babban birnin jihar.
“A halin yanzu ‘yan kwangilar sun riga sun isa wurin, kuma aiki ya kankama,” in ji shi.

About andiya

Check Also

Dangote Hails Tinubu on Impact of Crude for Naira Swap Deal

      …As Dangote Refinery partners MRS to sell PMS at N935 per litre …

Leave a Reply

Your email address will not be published.