Home / Labarai / Batun Zaman Lafiya Harka Ce Da Ta Shafi Kowa – Mai Mala Buni

Batun Zaman Lafiya Harka Ce Da Ta Shafi Kowa – Mai Mala Buni

Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Yobe kuma shugaban Kwamitin rikon jam’iyyar APC Mai Mala Buni ya bayyana cewa ya dace jama’a su daina mancewa da batun zaman lafiya al’amari ne da ya shafi kowa.
Mai Mala Buni ya bayyana hakan ne a cikin wani shirin tattaunawa da kafar Talbijin ta Farin Wata, inda ya ce ya dace a tuna fa babu wani da baya son a zauna lafiya a ko’ina yake a fadin duniya baki daya ba ma Najeriya kawai ba, don haka kowa ya Sani cewa akwai bukatar ya bayar da gudunmawarsa wajen batun samar da zaman lafiya.
Gwamna Mai Mala Buni ya kuma ce babu wata Jiha a Najeriya da bata fama da matsalar kudin Albashi ko na yan fansho ba don haka “korar ma’aikata ma wata matsalar ce daban wanda ya dace duk mai kallon hakan a matsayin mafita ya yi duba da kyau, a fili lamarin yake kananan hukumomi da yawa ba su iya biyan kudin Albashi, don haka dai kowa ya zama soja Malamin kansa kowa shi zai magance matsalarsa da kansa”, inji Mai Mala Buni.
“Akwai kuskuren wata sanarwar da wasu Gwamnoni suka fitar game da batun Fulani, don haka kada shugabanni su bari mabiyansu su rika yi masu tunani, kasancewa wasu daga cikin al’ummar Fulani a Kudancin kasar nan aka haife su ba su san ko’ina ba ban da Kudancin kasar, sabida haka batun a hana wasu uin amfani da dajin da Allah ya halitta hakika kuskure ne zalla domin in an yi hakan ya sabawa kudin tsarin mulkin kasar nan”.
Ya ci gaba da cewa duk masu kururuwar a sake Fasalin tsarin mulkin kasa ya na yin kuskure ne kawai domin a kai zuciya nesa ya fi duk kururuwar da ake yi.
“Masu tunzura jama’a ana maganganun da suka sabawa tsarin mulki ba za su yi nasara ba ko kadan”.
Hakika tattalin arzikin duniya ya shiga cikin wani hali, da ya Sanya kowace kasa na fama ne ta ga yaya za ta zauna da kanta.
Matsalar cutar Korona ta haifarwa duniya shiga cikin mawuyacin hali, saboda haka duk yan Najeriya su hada kansu domin kasa ta ci gaba.
Tin can baya an Jefa kasa a cikin wani hali amma a yanzu a zamanin mulkin Buhari ana kokarin a fitar da kasar cikin halin da ta  shiga
Ya kuma dace kowa ya Sani cewa babu wani yanki a Najeriya da ba ya bukatar wani yanki don haka kowa idanunsa su bude ya bayar da gudunmawarsa kasa ta ci gaba.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.