Home / Labarai / Bayan Zina Da Wata Yarinya Samari Sun Yada Faifan Bidiyon Tsiraicin

Bayan Zina Da Wata Yarinya Samari Sun Yada Faifan Bidiyon Tsiraicin

Bayan Zina Da Wata Yarinya Samari Sun Yada Faifan Bidiyon Tsiraici
Imrana Abdullahi
Shugaban Hukumar Hizba na Jihar Sakkwato Dokta Adamu Bello Kasarawa, ya tabbatar da samun wani faifan bidiyon wata yarinyar da saurayi ya lalata kuma abokanansa suka yada bidiyon.
Sanadiyyar yada bidiyon ya haifar da lalacewar maganar Auren yarinyar da suka yada faifan bidiyon.
Hakika faruwar yada bidiyon yasa wanda zai Aure ta cin tuwon fashi game da auren.
Adamu Bello Kasarawa ya bayyana cewa hukumar ya zuwa yanzu tayi nasarar kama dukkan mutanen uku, wato wanda ya aikata masha’a da budurwar lokacin tana da shekaru 17 da abokansa guda biyu.
“Mun samu nasarar kama wanda ya dauki yarinyar a shekarar 2017 da ta gabata ya kai wani Otal ya kwanta da ita ashe a lokacin ya dauki faifan bidiyonta tsirara kuma ya aikawa abokansa su biyu”.
Kasarawa ya ci gaba da bayanin cewa lokacin da ya aikata wannan aiki da budurwar a Otal yana da shekaru 18 ita kuma yarinyar tana da shekaru 17, an kuma aikata hakan ne a shekarar 2017 wanda a halin yanzu shekaru kusan uku kenan da aka aikata lamarin, kuma yaron a yanzu na da shekaru kusan 20 ita kuma yarinyar kusan 19 kenan, kamar yadda Dokta Bello Kasarawa ya bayyana wa kafar yada labarai ta bbc hausa a wata zantawar da suka yi sakamakon faruwar lamarin.
Dokta Bello Kasarawa ya ci gaba da cewa “Mun samu nasarar kama dukkan mutanen uku da wanda ya aikata abin da abokansa da ya aikawa da faifan bidiyon badalar da ya aikata da yarinya, dukkansu kuma sun tabbatar da aikata abin da suka yi su yaran biyu sun yada bidiyon da ya aika masu ne bayan da suka aikata abin da suka yi a dakin Otal, wanda sanadiyyar wannan faifan bidiyo na tsiraici wanda zai aureta ya fasa baki daya.
” Mun samu koke ne daga Uwar yarinya a game da abin da ya faru, nan da nan muka shiga aikin kamo wadanda ake zargi kuma sun bayyana mana cewa sun aikata abin da ake zarginsu dashi”.
Kasarawa ya ce sun mika batun yin zina ga hukumar NAPTIP sai kuma suka mika lamarin wadanda suka yada bidiyo ga hukumar tace Fina finai ta Jiha duk domin su dauki matakin da ya dace bisa doka.
Sakamakon aikata wannan lamari dai na yada faifan bidiyon a kafofin Sada zumunta na zamani wanda tushen lamarin Baffa Hayatu Tafida ne ya aikata ya haifar da lalacewar maganar auren da aka shirya yi a ranar 17, ha watan Okutoba, 2020.

About andiya

Check Also

Union Across River Niger: New Nigerian Editor Brother’s Wedding Grounds Makurdi

    Makurdi the capital of Benue State was agog all through the weekend, as …

Leave a Reply

Your email address will not be published.