Home / Labarai / Boko Haram, sun sake kashe masu Sana’ar Tarawa Da Sayar Da Tsoffin Karafa 20 A Borno

Boko Haram, sun sake kashe masu Sana’ar Tarawa Da Sayar Da Tsoffin Karafa 20 A Borno

 

Daga, Sani Gazas Chinade, Maiduguri

 

 

Wasu maharan da a ke kyautata zaton ‘Yan Kungiyar Boko Haram /ISWAP ne sun halaka wasu masu sana’ar tarawa da Sayar da tsoffin karafa da ake wa lakabi da’ yan Ajakuta ko ‘yan jari Bola su kimanin 20 a Dikwa cikin Jihar Borno.

 

Wata kwakkwaran majiya ta ce wasu mazauna garin sun bar sansaninsu na yau da kullun da ke kewayen kauyensu inda suka bi tazarar kilomita da dama bayan yankin da aka tanada don yin fatali da kayan karafa, sai kawai suka fuskanci ‘yan tada kayar baya wadanda su ma suke taruwa domin neman kudi.

Wasu majiyoyin civilian JTF da suka zanta da manema labarai sun yi ikirarin cewa sun samu nasarar tattara gawarwaki kusan 20 nan take suka garzaya wurin da aka kai harin a wannan ranar kai harin don ganewa idon mu nan ta ke muka gano cewar  adadin ya kai 25 kuma dukkansu sun mutu ne ta hanyar harbe-harbe da aka yi a kusa da wajen da kuma yankan rago.

Wannan majiya ta Civilian JTF da ke da hannu wajen kwashe gawarwakin tare da Dakarun  Sojoji ta shaida wa manema labarai cewa an yiwa wadannan mutane  masu fasa karafa  kisan gilla ne  a kauyen Boboshe Mukdala na Dikwa.

“Yayin da nake magana da ku mun kwashe gawarwaki 25 daga wurin wadanda aka harbe su gaba daya.  Kamar dai yadda muka gano gawarwaki kimanin da kuma tarkacen karafa daga inda aka kai harin.”

“Mun hadu da wasu da ransu da raunukan harsashi.  Sai da muka garzaya da su babban asibitin garin Dikwa tare da hadin gwiwar sojojin Najeriya domin ceton rayukansu,” inji majiyar.”

“A bayyane yake cewa bayan sun harbe su, an yi musu yankan rago.  Akwai yara a cikinsu, Boko Haram kafirai ne,” in ji wani mazaunin garin da ya tsira da ran sa ya bayyanawa manema labarai.”

“Malamin da ya nemi a sakaye sunan sa ya kara da cewa, Sun zo ne a kan babura uku kowanne dauke da mutum uku sannan suka kewaye mu da manyan bindigu kafin su fara harbe-harbe kan  mu tare da kashe kusan dukkan abokan aikina da ke wurin tare da kwashe tarkacen da aka fi sani da Ajaokuta,” inji shi.”

Shi ma wani ganau da ya zanta da manema labarai ta wayar tarho ya ce  “Ni ma dan kauyen Malamkari ne, ban iya tantance baburan nawa suka hau ba amma na ga mutane suna gudu don neman mafaka a kauyen.”

“Ya ci gaba da cewa, daga nan ne maharan suka bukaci kowa ya dawo, wasu kuma suka yi biyayya bayan haka na fara jin karar harbe-harbe daga inda na buya a karkashin gada.  A lokacin da na bar maboyata don duba abin da ya faru a lokacin da suka bar wurin sai na ga gawawwaki kawai.”

Da yake mayar da martani kan lamarin wani Kwamandan sojan da ke yaki da Boko Haram Manjo Janar Chris Musa ya bayyana kashe-kashen a matsayin “Mummunan abu abin ki”

“A cewar kwamandan Mun aika da sojoji domin su taimaka wa mutanen yankin wajen kwato gawarwakin.  Mun kwato gawarwaki 20 a ranar amma tun farko ‘yan Ajakutan an ba su iyaka da kada su ketare don kare lafiyar su.  Amma galibi suna shiga cikin dazuzzuka inda suke haduwa da masu tayar da kayar baya suma suna kwashe karafa hakan ne ta faru yayin da suka hadu da su, su kuma Suka  kashe su yayin da wasu daga cikin su Allah ya ba su dama suka tsere

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.