Home / Labarai / Borno Wuri Ne Mai Ingantaccen Tsaro Fiye Da Shekarun Baya – Farfesa Marte

Borno Wuri Ne Mai Ingantaccen Tsaro Fiye Da Shekarun Baya – Farfesa Marte

 Imrana Abdullahi
Shugaban ma’aikatan fadar Gwamnatin Jihar Borno Farfesa Isa  Husseini Marte, ya bayyana Gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum a matsayin hazikin shugaba mai rikon gaskiya da Amana tare da aiki tukuru.
Farfesa Isa Marte ya bayyana hakan ne a cikin wani shirin tattaunawa da aka yi da shi na gidan Talbijin na kasa “NTA” a shirin mai suna barka da Safiya.
Farfesa Isa Marte ya ci gaba da cewa manya manyan ayyukan da Gwamna Babagana Umara Zulum ya aiwatar sun fi dari 556 da aka rubuta a cikin lissafi domin da akwai wadansu ayyukan da aka hade su cikin wasu a wajen lissafi don haka aikin da wannan jajirtaccen shugaba ya aiwatar na da yawan gaske kuma a cikin kankanin lokacin da ya yi ne a matsayin Gwamna a Jihar Borno.
Farfesa Marte ya kara da bayanin cewa Jihar Borno a halin yanzu ta kasance wuri ne “mai cikakken ingantaccen tsaro, fiye da irin yadda lamarin ya kasance a can shekarun baya ba”.
“A bisa samun wannan nasarar muna kara yi wa Allah godiya da ya ba mu wannan jajirtaccen shugaba a matsayin Gwamna a Jihar Borno da ayyukansa da jagorancinsa ke kara wa duniya karfin Gwiwar cewa Borno jiha ce da kowa zai iya zuwa ya gudanar da harkokinsa na rayuwa ba kamar yadda lamarin ya kasance can baya ba”.
“Mun gyara makarantun da ke daukacin kananan hukumomi, mun gida makarantu manya manya da za su dauki dalibai a kalla dubu 1500, mun gina guda 66 a cikin Jihar Borno domin karuwar al’umma baki daya”.
Gwamnatin Jihar Borno karkashin Babagana Umara Zulum ta kasance Jiha ce da Gwamnatin ci gaba daga Gwamnatin Sanata Shattima, don haka mun samar da abubuwan ci gaban rayuwa da yawa da suka hada da koyawa jama’a ayyukan sana’o’in da kowa zai dogara da kansa, ayyuka a bangaren kula da lafiyar jama’a tare da bunkasa harkar ilimin Jihar baki daya da suka hada da daukar karin ma’aikata da dai sauran dimbin ayyuka da dama.
A game da batun kungiyoyin bayar da magani ga masu bukata musamman yan gudun hijira dole sai sun shiga wani tsarin da Gwamnatin Jiha ta bullo da shi in ba haka ba to, duk wanda ba zai iya shiga cikin tsarin da Gwamnatin Jiha ta fito da shi ba sai dai ya kama gabansa, saboda mun gaya masu cewa babu yadda za a yi wata kungiya ko masu bayar da agaji zai rika kaiwa yan Ta’adda magunguna a ce wai an bayar da agaji babu wannan batu sam”. Inji Marte.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.