Daga Sani Gazas Chinade, Maiduguri
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya sauka a filin jirgin sama na bangaren Sojojin Sama da ke Maiduguri, Borno domin ziyarar aiki ta kwana daya.
Jirgin shugaban kasa wanda ya sauka da misalin karfe 12 na rana cikin tsauraran matakan tsaro da kuma ruwan sama ya samu tarba daga gwamnan jihar Borno Babagana Zulum da dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Kashim Shettima, Sanata mai wakiltar Kudancin Borno, Ali Ndume da sauran manyan baki.
Yayin da al’ummar Borno ke tarar sa shugaban kasar sai ya zar ce kai zuwa sabon rukunin gidajen malamai da aka gina a unguwar Bulumkutu a cikin babban birnin jihar inda ya kaddamar da aikin da gwamnatin Gwamna Zulum ta aiwatar.
Wannan rukunin gidaje na malamai ya ƙunshi gidaje 24 a tsakanin duplex shida, don sadaukarwa ga malaman makaranta, yana ɗaya daga cikin manyan ayyuka sama da 600 da aka aiwatar a cikin shekaru uku na gwamnatin Zulum, waɗanda, mafi yawan waɗannan ayyukan shugaba Buhari ne ya kaddamar da su.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, nan da nan bayan kaddamar da rukunin gidajen malaman shugaba Buhari ya zarce zuwa fadar mai martaba Shehun Borno, Dr. Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin Elkanemi domin kai ziyarar ban girma da kuma samun albarka.
Ziyarar ta Buhari dai ta zo sai-dai ne da tunawa da ranar jin kai ta duniya ta 2022 ta hanyar kaddamar da tallafin jin kai ga dubban iyalai da ke gudun hijira da sauran marasa galihu a jihar.
Har ila yau, a yayin ziyarar, zai kaddamar da gidaje 500 na sake tsugunar da ‘yan gudun hijira a yankin Molai wadanda ke cikin gidaje 10,000 na sake tsugunar da masu Gudin Hijira a halin yanzu da shugaban kasa ya amince wa jihar Borno da sama da gidaje 6,000 da ya zuwa yanzu an kammala su, kuma an ware su ga wadanda suka amfana da su