Home / Labarai / BUHARI YA NUNAWA BOLA TINUBU YADDA FADAR SHUGABAN KASA TAKE

BUHARI YA NUNAWA BOLA TINUBU YADDA FADAR SHUGABAN KASA TAKE

Daga Imrana Abdullahi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari mai barin gado, a ranar Juma’a ya kai wa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu a wani rangadin sanin makamar aiki a fadar shugaban kasa da ke Abuja, wanda hakan zai ba sabon zababben shugaban mai jiran rantsuwa sanin yadda fadar take.

Buhari da Tinubu sun isa dakin taron manema labarai da misalin karfe 1:18 na rana jim kadan bayan kammala Sallar Juma’a a masallacin fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Inda shugaban mai barin Gado ya ce “Wannan ita ce Taswirar inda za ku gana da ‘yan jarida,” Buhari ya shaida wa Tinubu yayin da mutanen biyu suka fito daga dakin jira na fadar shugaban tarayyar Najeriya”.

Wannan dai na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da shugaban kasar ya bai wa Tinubu lambar girmamawa ta kasa ta Babban Kwamandan Tarayyar Najeriya da kuma Babban Kwamandan da kuma wata babbar lamba ga zababben mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, a wani dakin taro na da yake fadar ta shugaban kasa duk a jiya.

A ranar Alhamis ne mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kai wa Shettima ziyara har suka yi rangadi a fadar shugaban kasa.

A wanann hoton za a ga lokacin da shugaba mai barin Gado ke yi wa Tinubu jawabi a kan kujerar mulki da taurin shugabanci

Shugabannin biyu sun yi musayar takardu gabanin mika mulki a hukumance a ranar Litinin, 29 ga Mayu, 2023.

A lokacin da suka kammala tattaunawarsu Tinubu zai koma daga fadar

About andiya

Check Also

Dangote cement export of clinker, cement increase by 87.2%

  Management of Dangote Cement Plc has revealed that the company dispatched seven ships of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.