Home / Labarai / Sanata Muktar Dandutse Ya Tallafawa Yan Kasuwar Funtuwa Da Miliyan Goma

Sanata Muktar Dandutse Ya Tallafawa Yan Kasuwar Funtuwa Da Miliyan Goma

 

Daga Imrana Abdullahi

Bayanan da muke samu daga Jihar Katsina na bayanin cewa Sanatan yankin Funtua za a jihar Katsina Sanata Muntari Dandutse Funtua, ya taimakawa yan kasuwar Funtuwa da suka samu matsalar jarabawa ta yin Gobara wanda sakamakon hakan suka yi asara mai dimbin yawa.

Ya dai cika alkawarin da ya yi na bada kudi Naira miliyan Goma (10.million) ga yan’ kasuwar funtua Wadanda suka yi gobara a makon da ya gabata.

Ajiya lahadi ne 28-april-2024 Mai girma Sanata Muntari Dan’dutse Ya yi wannam alkawari na bada gudunmuwar Naira miliyan goma ga yan kasuwar
Bayan ziyarar da ya kaima masu da kanshi har cikin kasuwar domin ya yi masu jaje a kan iftila’in gobara da ya faru dasu

A yanzu haka Mai girma Sanata Dan’dutse ya bada wadannan Kudi’ yau litinin kamar yadda ya yi alkawari

Kuma kamar yadda muke samun bayani tuni kudin sun shiga hannun kungiyar kasuwa yanzu haka
Inda babban jigo Malan Atiku Dikke ne ya jagoranci kawo waannam kudi.

Muna addu’ar Allah ya sakama Sanata Dandutse da alkairi bisa ga irin wannan kokari da ya ke yi na tallafama al’ummar mazabar shi domin su ci gaba da yin rayuwa cikin kwanciyar hankali.

About andiya

Check Also

INSECURITY: GOV. LAWAL COMMENDS TROOPS OVER RENEWED ONSLAUGHT AGAINST BANDITS, EXPRESSES SYMPATHY FOR AFFECTED COMMUNITIES

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has commended the Joint Task Force for the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.