Home / News / Bunkasa Noma: Za A Raba Najeriya Da Talauci – Injiniya Bana Kachallah

Bunkasa Noma: Za A Raba Najeriya Da Talauci – Injiniya Bana Kachallah

Daga Imrana Abdullahi

An bayyana mataimakin Shugaban kasa Sanata Kashim Shettima a matsayin wanda zai yi kokarin warware matsalar da manoman Najeriya ke ciki sakamakon fahimtar da ya yi da yanayin da suke ciki

Kuma ya fahimci cewa idan ba a samu taimakawa Juna ta hanyar yin aikin kai da kai ba, domin talauci na da fuskar arewan kasar nan kuma yankin arewannan ya fi kowa talauci don haka dole sai an tashi tsaye domin yaki da talauci domin kada wankin hula ya kai mu Dare.

Injiniya Baba Kachallah ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan kaddamar da bayar da tallafi da horas da mutanen da aka zaba da za a Koyar a kuma ba su tallafin kayan Noma da Gidauniyar Kashim Shettima ta dauki nauyi wanda mataimakin shugaban ya kaddamar.

Injiniya Baba ya ci gaba da cewa ” Alhamdulillah an samu shugaba mai basira da fasaha da ya mayar da hankali wajen karfafa matasa domin su shiga harkar Noma, ku duba fa Tarakta huda daya fa naira miliyan Hamsin ne amma fa Mataimakin shugaban kasa ya samar da guda Goma ne fa da dukkan matasa masu da suka samu horon koyon Noman nan su Hamsin za a ba su Tarakta daya kuma ba za a bar su haka ba an kawo masana ilimin Noman kansa da za su tantance irin kasar Noman ko ta dace da abin da za a shuka? Idan aka shuka tsirowar da amfanin ke yi ba a samun tangarda? Idan da akwai ciyawa ga maganin ciyawar an kawo duk za a ba su kyauta, kuma idan an yi gurbin amfanin ga kasuwa an sama masu ga mutane nan sun zo daga Rasha da Belarus suna bukatar abubuwan da za a shuka ga kuma amfanin da zai yi mana a cikin gida mu kan mu nan duk da nufin ayi maganin hauhawar farashin kayan abinci. Kaga dai an hau kan turbar inganta harkar Noma da kuma raba arewacin Najeriya da talauci”.

Mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima a lokacin da yake duba kundin bayanan Noma a wajen kaddamar da horas da matasa 50 a kowace cikin Jihohi 10 da aka zaba na Gwaji

Misali kamar irin taimakon da Gwamnati ke yi akwai abin da ake cewa ga shi nan daki daki, “sai kawai a takaita lamarin a wani gurbi kawai. Amma a wannan tsarin na Mataimakin shugaban kasa mai son jama’a an yi la’akari da duk abin da za a yi ne kaco kam dinsa tun daga shuka zuwa kasuwar da za a sayar da kayan amfanin da za a Noma mutum Hamsin kowane jiha guda Goma da za a fara da su da a lokacin bayar da horon za a rika ba su kudin Jeka ka dawo na dubu dari dari har watanni hudu daga cikin shidan nan”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.