Home / Labarai / Burina Ciyar Da Duniya Abinci. – Ibrahim Nyauri Buba 

Burina Ciyar Da Duniya Abinci. – Ibrahim Nyauri Buba 

Daga Imrana Abdullahi
Tsohon mai shari’a Ibrahim Nyauri Buba,Walin Mambilla,Turaki Gashaka na masarautar ƙaramar hukumar Sardauna ta Jihar Taraba, kuma Majidaɗin matasan Arewa, ya ce duba da halin da ake ciki a ƙasa,burinsa shi ne ya ciyar da duniya da abinci ba kawai ƙasa Nijeriya ba.
Ibrahim Nyauri Buba,ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan amsar lambar karramawa daga Ƙungiyar Mawallafa Jaridu da Mujallu ta Arewacin Nigeriya mai suna  “Arewa Publisher’s Forum” wanda ya gudana a ƙarshen makon da ya gabata, a gidan gonarsa da ke kan titin filin Jirgin sama,Mando,Kaduna.
Ya ce ina muku maraba da zuwa gidan gonar (Buba Integrated farm) tun da yanzu na riga na yi ritaya daga aikin shari’a,yanzu nan ya zama gidana,duk wanda ya sanni ya san ni da Noma da Kiwo ne.
“Burina shi ne inga mun ciyar da duniya da abinci ba kawai ƙasa  Nijeriya ba,kuma yanzu na dawo domin bayar da gudunmuwa ta wannan fannin.Inji shi.”
Mai shari’a Ibrahim Nyauri Buba  ritaya,ya nuna farin cikinsa da godiya ga Allah madaukakin sarki da ya nuna mashi irin wannan rana, wanda ƙungiyar suka ga ya cancanta da su karrama  shi da lambar girmamawa.
“duk lokacin da aka bani lambar yabo,abun tambaya shi ne,shin na can canta abani,in kuma na cancanta, to na cancanta. Maganar mutane shi ne maganar Allah.’ kamar yadda ya bayyana.
Tsohon mai shari’a Buba ya ce a saboda haka, ina so inyi amfani da wannan dama  wajen godewa mai martaba Sarkin Gashaka da ya sami halartar wannan taro da kuma bukin ɗansa da kuma jikansa.
Kazalika,a ɓangare ɗaya kuma Mujallar Dome ta majalisar wakilai,mai suna “Dome Assembly magazine”ta miƙa wa mai shari’ah Ibrahim Nyauri Buba mai ritaya lambar yabo duk a ranar kuma a lokacin.
Da take zantawa da manema labarai ƴa ga mai Shari’a Bilkisu Ibrahim Buba ta bayyana farin cikin ta da godiya ga Allah madaukakin Sarki bisa wannan abun farin ciki da ya same su da mai martaba Sarkin Gashaka, Dokta Zubairu Hamma Gabdo Lamiɗo bisa halartar bikin ɗan uwanta.
Ta kuma ƙara da cewa gonar (Buba Integrated farm)ba manufar samar dashi shi ne don wadata ƙasa da abinci kawai ba ne,ganin cewa Noma shi ne tushen arziki kuma ci gaban kowacce ƙasa.
Ta na mai cewa, “ina farin ciki da kuma alfahari da manufar mahaifin na kan abin da ya shafi Noma da kiwo”.
Wasu daga cikin mahalarta taron karramawar kenan a lokacin Karrama Mai shari’a Inrahim Nyauri Buba da mai martaba Sarkin Gashaka
Da yake magana a madadin ƙungiyoyin da suka bada lambar yabon, Mataimakin shugaba na ƙungiyar Mawallafa Jaridu da Mujallu na Arewacin Nigeriya mai suna “Arewa Publisher’s Forum”Dokta Sani Garba ya ce sun bashi lambar yabon ne bisa taimakon al’umma da kuma  jajircewa wajen gudanar da shari’a bisa kan gaskiya da riƙon amana lokacin da ya gudanar da aikin sa.
Har ila yau,Karramawar na zuwa ne bayan da mai Shari’a Ibrahim Nyauri Buba mai ritaya ya aurar da ɗansa duk a ƙarshen makon,taron da ya sami halartar manyan mutane, Sarakuna,ciki har da Sarkin Gashaka, Dokta Zubairu Hamma Gabdo Lamiɗo na Jihar Taraba.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.