Home / KUNGIYOYI / Tajudeen Ibikunle Baruwa Ne Halastaccen Shugaban NURTW Na Kasa – Tanimu Zariya

Tajudeen Ibikunle Baruwa Ne Halastaccen Shugaban NURTW Na Kasa – Tanimu Zariya

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna

An bayyana Tajudeen Ibikunle Baruwa, a matsayin halastaccen zababben shugaban kungiyar direbobi ta kasa NURTW da aka zaba ta hanyar bin ka’ida da tanajin kundin tsarin mulkin kungiyar.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin sabon mataimakin shugaban kungiyar na kasa kuma shugaban NURTW na Jihar Kaduna Alhaji Aliyu Tanimu Zariya, a lokacin wata zantawarsa da manema labarai a ofishin kungiyar da ke Kaduna.

Alhaji Aliyu Tanimu Zariya ya ce hakika halastaccen zababben shugaba na kasa shi ne Tajudeen Ibikunle Baruwa, da aka zaba a kan tafarkin tanajin tsarin mulkin kungiyar.

“Ina yin kira ga daukacin yayan kungiya ga duk wanda abin bai yi masa dadi ba to, a dauki matakin doka domin samun maslaha da ake bukata. Saboda haka ne nake yin kira ga yayan kungiyar na can kasa da su ci gaba da zama masu yin biyayya ga kungiyar kada kuma su sake wani ko wasu ya Sanya su yin abin da ya saba wa ka’ida domin a samu sukunin neman abincin da ake yi cikin walwala da jin dadi”.

Kamar yadda Alhaji Aliyu Tanimu Zariya ya shaidawa manema labarai cewa hakika shi ne zababben mataimakin shugaba na kasa kuma Tajudeen Ibikunle Baruwa ne shugaba kungiyar NURTW na kasa.

Kamar dai kowa ne lokacin zabe in ya yi “kowa ce shiyya ana yin tsarin zabe kamar dai yadda yake a cikin kundin tsarin mulkin kungiya, bisa yanki yankin da ake da shi a Najeriya guda shida hakan ta Sanya a wannan yankin na mu sai muka gudanar da zabe kuma akwai hedikwatar yankin Arewa maso Yamma a Jihar Zamfara kuma a nan muka je muka zauna aka fitar da tsarin zabe kuma aka turo masu zabe daga hedikwatar kungiya ta kasa aka tabbatar da an zauna da kowa ne shugaba na Jiha, sakatare, ma’aji na dukkan Jihohi Bakwai. Ni kuma a wannan kujerar da na samu ta mataimakin shugaba na kasa na same ta ne tun bayan da shi wanda yake kanta ya ta fi neman shugabanci na kasa sai kuma kujerar Odita (Auditor) kujera ce wadda ada can Alhaji Yahuza Yan kaba ke kanta sai shi shugaban kungiya na Jihar Jigawa ya fito tare da goyon bayan shugabannin wannan yankin da suka hada da shugaba, Sakatare, ma’aji da dukkan deliget guda biyu daga kowace Jiha a wannan shiyya duk sun bayar da cikakken hadin kai da goyon baya a matsayin su na masu hakkin zabe kamar yadda kundin tsarin mulkin kungiya ya tanadar sun nuna goyon baya ga Alhaji Danjuma Babura Jigawa da Alhaji Yahuza Alhaji Yawale da Alhaji Dan Auwade suka fito takara duk suka taru suka janye takararsu a kan Alhaji Danjuma Babura sai kuma maganar amintaccen kungiya wato turosti, da yake a can baya akwai Alhaji Ibrahim Kuka Lere Guga wanda shi dan Zamfara ne ke kan kujerar kuma bangaren su shugabanni suka fitar da Alhaji Hamisu Kasuwar Daji sai aka tabbatar masa da kujerar turosti kamar yadda doka ta bayar da dama aka yi deliget aka tabbatar da hakan.

Wannan shi ne Tajudeen Ibikunle Baruwa da ake wa lakabi da Furofesa halastaccen shugaban kungiyar NURTW na kasa

Aliyu Tanimu Zariya ya shaidawa manema labarai cewa irin wannan hakan aka yi a kowane yanki a dukkan sassan kasar nan baki daya aka kuma ajiye cewa idan Allah ya kai mu a ranar Ashirin hudu ko a Ashirin da biyar na wannan watan za a tabbatar da an kaddamar wato an Rantsar da dukkan shugabannin baki daya da aka zaba kamar yadda tanajin tsarin mulki ya tanadar. Kuma hakan ya sa aka kira taro a Jihar Nasarawa kuma a can muka taru duk Jihohin 34 da suka halarci wannan gagarumin taro ciki har da Abuja kuma ni kaina ina daya daga cikin wadanda suka halarci wurin da aka Rantsar da shugaba wato Tajuseen Ibikunle Baruwa a matsayin shugaban kungiyar NURTW na kasa tare da sauran mukarraban da aka zabo a matakin shiyya wato mu kenan da Sakatarori da ma’aji Ma’aji duk tare da deliget da suka taru a wannan wurin.

” Don haka mu a yanzu shi ne wato Tajudeen Ibikunle Baruwa muka Sani a matsayin shugaba muka Sani matsayin shugaba ba mu san kowa ba sabanin sa ba da ikon Allah”.

Tanimu Zariya sai ya kara da fadakar da jama’a cewa kamar yadda dai kowa ya sani a duk lokacin da aka yi zabe za a samu wasu Suga cewa abin da aka yi bai yi ba wasu kuma su bi gaskiya su ce ya yi dai- dai. Ni dai abin da na Sani koda a Gwamnatin kasa ne da kuma jam’iyyun siyasa idan aka ce akwai wata matsalar da aka samu a wajen gudanar da zabe ko wani yaga an yi wani abin da yake yi bai Gamsu ba, ba wai daukar doka a hannu mutum yake yi ba kawai abin da ake yi mutum zai tattara abin da yake gani hujja ne a hannunsa ya ta fi kotu kawai domin ita kotun ce za ta iya fitar wa da mutum hakkinsa da yake ganin an yi abin da bai dace ba a nasa ganin.

Ya kara da cewa batun kaiwa da dawowa nan muna sane da wadanda ke ganin abin da aka yi bai dace ba wato tabbatar da Tajudeen Ibikunle Baruwa a matsayin shugaba su ba abin da suke bukata ba ne hakika wannan ra’ayin su ne kawai. Jihohi dai da ya kasance muke da kuri’u da kuma deliget kuma muke yin zaben ga abin da muka zaba a dukkan mataki da muka fitar da shugabanci bisa tsarin kundin mulkin kungiya.

” ina jan hankali ga daukacin yayan kungiya na Jihohi dukkansu da su ci gaba da sanin cewa wannan kungiya ce da ke da albarka kuma ta na dauke da dimbin al’umma masu yawa da suke cin abinci a karkashin ta don haka wadanda suke yi shugabancin suka gama kuma a lokacin da suke yin shugabancin an Kyale su sun yi shi sun kuma zauna lafiya don haka ya dace a yanzu su kyale wadanda ke shugabancin su zauna lafiya shi ne ci gaba kungiya da yayanta tare da kasa baki daya.

Sannan su mambobi su zama masu biyayya ga shugabanni domin idan sun yi biyayyar zai taimaka ana zaune lafiya, amma matukar wanda ke kasa wannan rigingimu lamari ne da ya taso na hedikwata ta kasa don haka kai da kake kasa a wani yanki ko biranci rigima ba taka ba ce kai dai fatanka kawai yin addu’a da fatan alkairi Allah yasa duk wata matsalar da ta taso ai muna ganin rigingimun siyasa ma na Gwamnati duk ya na zuwa ya wuce haka ma na kungiya irin wannan ana yin sa ya wuce da haka ne muke fatan Allah ya shige mana gaba ya yi mana jagora kuma dukkan wadanda ke neman kawo mana wani sanadi a kungiyar nan Allah ya fi mu saninsu zai yi mana maganinsu.

Mataimakin shugaban na kasa Aliyu Tanimu Zariya ya kuma yi kira ga hukumomi cewa kamar yadda aka Sani dadlilin kafa hukuma shi ne domin tabbatar da zaman lafiya da tsare rayukan al’umma da dukiyarsu saboda haka idan an samu wasu na yin kutse su tayar da tashin tashina to, muna kira ga dukkan hukumomin jami’an tsaro da su Sanya idanu a kan irin wannan da nufin haka cin mutuncin wani ko yin amfani da wata dama a barnata dukiyar al’umma ko a kawo wata hatsaniya don haka muke kira da su dauki mataki ga duk wanda bai Gamsu da abin da aka yi ba ya wuce ya je kotu ba ya tsaya ya ce zai tara mutane ana hayaniya ko ana fashe fashe ko ana jefe jefe ba har ya shafi wanda ma ba ruwansa. Muna zaune lafiya a kasar mu da Jihohin mu don haka duk abin da zai kawo rigingimu da aka fara shi a kasa ayi wa tukka hanci.

“Alhamdu lillahi, ita wannan kungiya tun daga matakin kasa zuwa na jiha a nan Kaduna gaskiya muna da matakai da yawa kuma Kona wannan wurin a sakatariyar kungiyar mu ta Jiha muke ba gidan haya ba  kungiya ta mallaki wurin saboda dukkan shugaban da yazo ya na yin wani abu ne na ci gaban kungiya domin ya bari kungiya ta ci gaba da amfana a samu ci gaba saboda haka ne shugabannin da suka gabata suka kafa Harsashin ginin wannan wuri har muka zo bayan nan muma mun kara wadansu abubuwa a gidan kun gani mun yi gidan Ruwa mun bude bangaren sufurin motoci a samawa kungiyar kudin shiga sannan kuma muna ta kara jawo sauran wadanda suka ta ba yin shugabanci duk mun jawo su muna hade domin ayi tafiya tare a samu ci gaban kungiya. Kuma akwai abin da muke tanada na isuwa ga shugabannin matakan rassa a duk shekara a bayar mun yi hakan a kalla kashi hudu kuma muna saran za mu yi hakan nan gaba da ikon Allah.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.