Home / MUKALA / Da Gaskiyar A’isha Buhari

Da Gaskiyar A’isha Buhari

Daga Imrana Abdullahi
Kamar yadda muke karantawa a wadansu jaridun yanar Gizo da kuma shafukan jama’a da dama na dandalin Sada zumunta cewa an ji harbi a wani wuri a fadar shugaban tarayyar Nijeriya, har muka karanta cewa fadar na fadin cewa abin da ya faru ba wani babban lamari bane wato dan karami ne duk saboda irin kokarin da uwargidan tarayyar Nijeriya Hajiya A’Isha Buhari ke kokarin ganin an fayyace gaskiya an kuma yi aiki da ka’idar da aka shimfida na mutum ya killace kansa tsawon sati biyu kamar yadda muka karanta a shafin jaridun yanar Gizo cewa ta gayawa wani na kusa da Shugaba Buhari ya killace kansa sakamakon tafiyar da ya yi zuwa garin Legas kamar yadda aka wallafa a rubuce.
Kasancewa babu wanda mace ko Namiji zai bari wani nasa ya cutu musamman a wannan lokacin da yake yaki da cutar Korona a duk fadin duniya cutar da ta lalata tattalin arzikin duniya wanda sanadiyyar hakan aka shiga cikin rudu da rashin tabbas a duniya baki daya.
Sakamakon irin sayayyar da ke tsakanin miji da matarsa yasa ita da kanta A’Isha Buharin ta dauki matakin cewa ya dace shi wannan bawan Allah da ke kusa da shugaba Buhari mai suna Sabi’u  Yusuf da Buhari ke yi wa lakabi da “Tunde” wato ya Gaji sunan marigayi tsohon mataimakin shugaban kasa Buhari a lokacin da suka yi shugabancin Nijeriya a mulkin soja.
Kasancewar Sabi’u Yusuf  Tunde a matsayin mutumin da ya samu nasarar kasancewa a kusa da shugaban kasar tarayyar Nijeriya Buhari, matsayin da shi kansa Sabi’u Yusuf din bai yi mafarkin zai kasance a kan irin wannan matsayin ba amma saboda kusancinsa da shugaba Muhammadu Buhari ya bashi wannan matsayin, hakika ya dace idan zai yi tafiya a zance na hankali idan Sabi’u Yusuf Tunde zai yi tafiya irin wannan zuwa Legas a cikin yanayin da ake ciki kamar yadda Gwamnatin da yake cin albarkacinta ta shimfida dokoki da ka’ida da kuma tanaje tanaje ya shaidawa shugaba Buhari ga abin da ya same shi ga dalilin da zai ta fi zuwa Legas.
Saboda sanin irin yadda A’isha Buhari ta san halin da wadansu dimbin mata a Nijeriya suke kasancewa a matsayin ba mataimaki sai Allah a duk lokacin da aka bar mace da yaya, wato idan rai ya yi halinsa.
Hakan tasa uwargidan shugaba Buhari ta sanar da shi Sabi’u Yusuf bukatar lallai ya killace kansa, wanda kamar a rahotannin da muke samu idan hakan ta kasance gaskiya cewa dogarin da ke tsaron uwargidan shugaban ta harba bindiga a lokacin da suke magana tsakanin Sabi’u Tunde da iyalin shugaban kasar, to za a iya cewa ya saba ka’ida kamar yadda dokar kasa ta tanada, amma duk hakan ta faru ne sakamakon kokarin da iyalin shugaban keyi na ganin an tsare lafiyar shugaban kasa musamman daga cutar Korona da ke yi wa duniya barazana.
Kuma kamar yadda aka Sani cewa cutar Korona na yi wa mutane masu yawan shekaru illa fiye da kowa har ta kaisu ga rasa rai, saboda haka su iyalin shugaban kasa sun fi kowa sanin muhimmancin lafiyarsa da rayuwarsa baki daya, don sun dauki matakin cewa mutumin da ya tashi ya ta fi Legas kamar yadda rahotannin da muka karanta a jaridu cewa yaje ne domin ganin matarsa da ta haihu a can Legas, bayan ya san akwai tsari da tanaje tanajen Gwamnati da suka bukaci kowa ya kula da kansa kada ya rika tafiye tafiye musamman su da suke tare da shugaban kasa
Kamar yadda lamarin yake yakansance Shugaban kasa tare da yan majalisar zartaswarsa koda za su yi taro ne irin na sati sati ko ma taron duniya na shugabanni saboda illar cutar Korona suna yi ne ta kafar sadarwar bidiyo mai hoto da kowa zai iya ganin kowa kuma su tattauna abin da za su tattauna da ya shafi kasa ko duniya baki daya, haka suma Gwamnonin Nijeriya sukan tattauna a tsakaninsu duk ta kafar bidiyo mai amfani da hanyar sadarwar yanar Gizo, saboda haka tambaya a nan shi ne me yasa shi ya yi wannan tafiyar zuwa Legas a wannan yanayi da Gwamnatin Buhari wanda Sabi’u Yusuf “Tunde” ya samu nasarar kasancewa a cikinta suka kafa doka da ka’ida amma kuma ya aikata hakan.
Ai ni a ganina idan ma har uwargidan shugaban kasa A’Isha Buhari ta ce masa ya killace kansa tsawon sati biyu ai ba wani abin sai an tayar da hakarkari bane, saboda ita A’Isha Buhari tare da mai gidanta Sato shi kansa shugaba Muhammadu Buhari sun fito fili sun gayawa duniya cewa an killace yarsu a lokacin da ta dawo daga kasar waje kuma an yi hakan ne nantsawon sati biyukamar yadda tsare tsaren suka tanadar, to in shi Sabi’u ya aikata hakan ai ya aiwatar da abin da Gwamnatin da yake ciki ya kuma amfana ko yake amfana da shimfida saboda abin da iyalin shugaban kasa ke gaya masa na ya killace kansa don yaje Legas abune da yake a kan hanya.
Kuma daman can an san uwargidan da kokarin gayawa mijinta gaskiyar cewa ita fa akwai na gaba gaba a cikin wannan Gwamnatin da Talakawa suka yi kokarin aka kafa karkashin Buhari amma ita a matsayinta na uwargidan shugaban kasa bata ma san su ba, kasancewarta wacce ta san wadansu da yawa da suka dade suna fafutuka a tafiyar Muhammadu Buhari amma bata ganin irin wadancan yan fafutuka a cikin Gwamnatin da mai gidan nata ke yi wa shugabanci.
Kuma wata matashiyar da za a yi wa na kusa da shugaban kasa Muhammadu Buhari Sabi’u Yusuf “Tunde” shi ne, shi da iyalan shugaban kasa Muhammadu Buhari ba daidai bane a ji su har sun kai ga cewa dole wane sai kayi kaza, Alhli abune da yake a kan doka da tsare ka’ida, kuma iyalin shugaban kasa idan sun yi wa Sabi’u magana ya dace ya amsa masu da ladabi da biyayya ko ba komai saboda shi mai gayya mai aiki shugaban kasar da ya kawo ka kake cikin Gwamnati.
Kuma suma masu kokarin cewa suna tsare dokar kasa ta hana a harba bindiga a fadar shugaban kasa su Sani fa iyalin shugaban suna yi ne domin kare lafiya da mutuncin su baki daya saboda duk wani mutum da aka nada a kowane irin mukami ne kai har ma da wasu da suka samu nasarar lashe zabuka daban daban duk an samu nasarar ne albarkacin shugaban kasa Muhammadu Buhari, bayan ya samu nasara sakamakon Gwagwarmayar talakawan Nijeriya sai yaga dacewar ya kawo su cikin Gwamnati, don haka A’Isha Buhari na yi ne domin kare mutuncin kowa saboda abin da ya taba hanci idanu sai su kama zubar da ruwa, kuma albarkacin kaza kadangare ke shan ruwan kasko, saboda haka abin da Aisha Buhari ta aiwatar yana kan hanya kuma tana da gaskiya kokari ne domin jama’a da yawa su ci gaba da amfana, Gaskiya sunanta kenan kuma bata neman Ado.
Ana Iya samun M Imrana Abdullahi a lamba kamar haka a whatsapp 0809727 3335 da kira ko sako a 080 3606 5909 ko a email shieldg2014@gmail.com

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.