Home / Garkuwa / Da Za’a Ratattake Masu Satar Mutane Da Bam Da Sai Tarihi – El-Rufa’I

Da Za’a Ratattake Masu Satar Mutane Da Bam Da Sai Tarihi – El-Rufa’I

Imrana Abdullahi

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i ya bayyana cewa da Gwamnati za ta yi amfani da sojojin sama su shiga cikin dazuzzukan da masu satar mutanen nan suke da za a yi maganinsu cikin lokaci.
Malam Nasiru ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa tambayoyin jama’a cikin wani shirin BBC hausa tare da hadin Gwiwar Gidauniyar Makasa.
Ya ci gaba da cewa shi da za a biye tasa a dauki matakin sojojin sama su shiga dazuzzukan da masu satar mutanen nan suke duk a zuba masu Bama Bamai da zai fi kuma Sauran jami’an tsaro su tsaya a baya duk wanda bam din bai same shi ba ya gudu saga inda ake ruwan bam din su gama da shi, amma matsalar ita ce kungiyoyin da ke cewa suna kare hakkin dan Adam
Inda wani ya tambaye shi ta yaya za a yi maganin masu satar mutanen da suke fitowa daga wuraren da aka koro su sai su shigo Jihar Kaduan.
“Mun taba zama Gwamnoni Takwas muka hada kudi miliyan dari dari kowace Jiha muka ba sojoji domin su shiga dazuzzukan da Barayin Shanu suke, ba shakka an yi maganinsu sai wadannan barayin mutane kuma suka taso kuma ana nan Gwamnonin jihohi da tarayya duk ana yin bakin kokari a kan wannan matsalar”.
Sai dai Malam Nasiru ya ce daga an dauki irin wannan matakin da yake magana na cewa a ratattake masu satar jama’a, yan kungiyoyi ne za su rika cewa an taka hakkin dan Adama har a rika cewa in kaje wata kasa ba kasarka ba a kama ka wannan shi ne gaskiyar lamari.
Kuma ya dace mutane su sani cewa ” Wata mafia ce da ta same mu kawai don haka ya dace a tashi tsaye a rika yin addu’ar neman kawo sauki da karshen abin daga Allah”.
Ya kuma bayar da albishir cewa nan bada komawa ba komai zai daidaita a kan harkar tsaro domin Gwamnati a matakin kasa da jihohi na nan suna gagarumin shirin kawar da matsalar tsaron

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.