Home / Big News / Dalilin Da Ya Sa Mutane Da Yawa A Kaduna Ta Tsakiya Suke Magana A Kan Shettima Yerima Kafin 2027

Dalilin Da Ya Sa Mutane Da Yawa A Kaduna Ta Tsakiya Suke Magana A Kan Shettima Yerima Kafin 2027

 

 

 

 

A matsayin batun tattauna wa a game da shekarar 2027 da sannu a hankali ke Kara kusantowa al’ummar yankin Kaduna ta tsakiya, wani suna ne da ke zuwa a gare du da a koda yaushe suke tattaunawa a kansa tsakanin Matasan,shugabannin al’umma da kuma lokacin tattaunawar yau da kullum sai dai kawai sunan Shetima Yerima Ake ji a ko’ina.

 

 

Wasu da dama, na wai kawai dalilin Siyasa ba ne kawai sai dai kawai samun ingantaccen wakilci, a samu murya da kowa zai tabbatar hakika an samu jagoran da ke kishin al’ummarsa.

 

Wato fuskar da aka Sani na wai irin wadanda kawaii daga sun zo na sai su bace don haka sunan Shettima Yerima BA sabon Abu ba ne a gare su, mutum ne da ya fito daga Zariya, cikin jihar Kaduna, kuma a tsawon shekaru an San Shi da yin fafutukar a Kan inganta rayuwar Matasa da kwato Yancin al’umma, a matsayinsa na shugaban kungiyar tuntubar Matasa a Arewacin Najeriya, ( AYCF),da aka Sani ya na yin magana a Kan abubuwan da suka shafi talakawan kasa musamman a Kan harkar tsaro, Samar da ayyukan yi,Hadin Kai da kuma samun kyakkyawan shugabanci na kamar dai yadda wasu Yan Siyasa suke BA.

 

 

 

 

Ba kamar wasu Yan Siyasa ba da kawai za a iya saninsu ne a lokacin da Ake yin hada hadar Siyasa, Shettima zai ci gaba da kasancewa tare da kowa a koda yaushe a tattauna abubuwan da suka shafi kasa musamman a wurin da Ake bukatar kare Yancin da ra’ayin Jama’a tare kuma da bukatunsu.

Me Yasa Mutane Ke Jin Lallai Yakamata Ya Wakilce Su

Yankin Kaduna ta tsakiya wurin ne mai cike da dimbin Jama’a daban daban masu bin addinai daban daban GA kuma ra’ayoyi maban banta. Mafi yawan jama’ar na cewa hakika wannan irin al’umma na bukatar Wanda zai Wakilce Su ya Zama mutum ne mai Sauran Jama’a, ya fahimce su ya kuma hada kansu ba wai rarra ba su ba.

 

Masu goyon bayan Shettima Yerima na cewa mutum ne da Jama’a ke iya gani da sauri domin ya kasance a tsawon shekaru ya na Hulda da Matasa,manya masu yawan shekaru da kuma kungiyoyin fafutukar kare hakkin Jama’a. Don haka ne suke cewa Shi ne Wanda ke fahimtar irin Hali da yanayin kuncin da Matasan da suka kammala karatun suke cikin da ke yawo na aikin yi, masu harkar kasuwanci kuma na fama da batun matsalar tsaro iyalai da yawa kuma na fatan samun damarmaki da yawa a rayuwarsa.

 

 

 

Murya ga Matasa,ba ma kawai GA Matasa ba domin Shi Shettima mutum ne da ya yi shura a farfajiyar Matasa musamman ta fuskar tuntubar, don haka ne ya dace magoya bayansa da su sani cewa Shiga irin tunaninsa da butin da Yake son comma ya wuce kawaii Matasa kawai.

Domin kowa ya sani irin kwarewar da Yake da ita ta wuce a wannan fagen kawai don haka ne ya samu damar yin ilimin Samar da dai daiton da Ake bukatar samu da zai yi WA kowa wakilci a yankin Kaduna ta tsakiya da ta hada Mata da Matasa Maza da Mata tsofaffin da yara.

 

 

A wani lokacin kuma da Yan Najeriya ke tambaya a game da samun ingantaccen Jagoranci da ya fahimci irin halin da Ake ciki a yau, irin yadda shettima Yerima ya dade ya na gwagwarmayar kwato Yancin Jama’a zai Kara bayar da kwarin gwuiwar Sosai, dalilin da kiraye kirayen ke Kara yawa suna ci gaba a kullum.

 

 

Haka ma a game da batun irin yadda Jama’a ke tattaunawa a kafafen sada zumunta na zamani muryoyi da yawa na karfafa wa Shettima Yerima Gwiwa da ya ci gaba da fafutukar Neman wannan kujerar ta Dan majalisar dattawa a shekarar 2027 mai zuwa. Dalilin kawai mai saukin ne,kamar yadda suke Fadi,”ya dade ya na yin magana a madadin al’umma a tsawon lokacin don haka me zai Hana ya yi magana a madadin mu a doron majalisar dattawa ta kasa?”

 

Masu nuna goyon baya sun yi Imani cewa irin yadda aka San Shi a matakin na kasa da kuma yadda tauraruwarsa ke haskawa duk za su taimakawa yankin Kaduna ta tsakiya su samu gagarumar nasara a majalisar dattawa da ke Abuja,kuma irin yadda Jama’a a matakin na can cikin al’umma za su samu biyan bukatunsu.

 

 

 

 

Idan aka yi duba da batun shekarar 2027 da ke Kara karatowa, masu zabe a yankin Kaduna ta tsakiya na Kara tunani mai zurfi a Kan irin shugabancin da za su samu. Wanda ya Zarce batun jam’iyyar, mutane da yawa na Tambaya: waye ya fahimce mu? Waye zai yi magana saboda mu? Waye za a iya gani koda zabe ya wuce? A Kan hakan Jama’a da dama na cewa lallai hakika Shettima Yerima ne za a samu duk wadannan abubuwan tartare da Shi.

 

 

 

KO ya kasance ya yi takarar KO A’a, hakika irin yadda a ko’ina Ake Jin sunansa wani Abu ne Mai matukar muhimmanci ,saboda yankin Kaduna ta tsakiya a shirye suke domin samun kyakkyawan sjagoranci da zai Kasance kusa da Jama’a da Yake da tausayi Jama’a kuma da BA zai ci amanarsu BA domin za a yi komai dalla dalla.

 

(Sagir Al-kasim)

About andiya

Check Also

Dangote headlines 2026 Gateway Trade Fair as Gov Abiodun hails Group for boosting Ogun’s Industrial Competitiveness

Ogun State Government has lauded the roles being played by the Pan-Africa conglomerate, Dangote Industries …

Leave a Reply

Your email address will not be published.