Home / Labarai / Dalilin Da Yasa Na Gabatar Da Kudirin Mata Masu Juna Biyu Da Bayan Haihuwa – Dan Abba Shehu

Dalilin Da Yasa Na Gabatar Da Kudirin Mata Masu Juna Biyu Da Bayan Haihuwa – Dan Abba Shehu

Bashir Bello Majalisar Abuja

Honarabul Dan Abba Shehu dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Zaki a Jihar Bauchi da ke arewacin tarayyar Najeriya ya bayyana cewa a halin da ake ciki a yanzu a kasar tarayyar Najeriya babu masu shan wahala kamar matan da aka mutu aka barsu da yara da kuma wadanda mazajensu ba su da komai kuma ga Juna biyu har lokacin haihuwa.

Dan majalisar ya ce ya na zuwa asibiti wajen duba marasa lafiya kuma ya na zuwa bangaren masu haihuwa lamarin da ke faruwa ba dadi ga masu Juna biyu da bayan sun haihu a asibitin.

Ya ci gaba da bayanin cewa sai kaga mace da ciki amma sai a rika neman samun matsala a tsakanin mace da mijinta domin kudin duba lafiyar mai cikin ko wajen haihuwa ko kayan haihuwa zaka ga mace na kuka abin ba dadi ko kadan.

“Saboda idan taje asibiti ba ta kokarin yadda za a raba ta da abin da take dauke da shi a cikinta ake ba sai ta yaya za a karbi kudi, hakika wannan abu ya daga Mani hankali kwarai sai na zo na yi nazari cewa wadannan mutane su suka yi mu musamman mata sun bamu gudinmawa wajen zabe don haka ne Naga ya dace in yi kira ga ma’aikatar lafiya da Gwamnati kanta baki daya kasancewar duk shekara ana ware masu kudi a cibiyoyin lafiya na kasa domin a taimakawa mata masu Juna biyu kafin su haihu da bayan sun haihu lokaci kadan. Wannan kudiri na yi shi ne domin ceton matan da kuma wadanda ba su da karfi dole ne Gwamnati ta duba ta yi sassauci ta bayar da magani kyauta ga haihuwar mace mai ciki da bayan ta haihukagin yayan su warware, wannan shi ne dalilin da yasa na yi kudirin”.

Dan Asabe Shehu ya kara da cewa kamar yadda aka Sani ma’aikatar lafiya na cikin wuraren da ke samun kaso mafi tsoka kuma akwai asibitocin Gwamnatin tarayya kuma akwai cibiyoyin duniya na lafiya da suke taimakawa don haka yakamata ace mata masu Juna biyu maganin haihuwarsu da bayan haihuwarsu duk ya zama kyauta, amma wasu yau abincin da za su ba su da shi ga wahalar Juna biyu ga kuma wahalar batun haihuwa da idan an zo ya za a yi idan kuma za a Karbe ka a wurin haihuwa a asibiti yaya za a yi sai fa mutum na da kudi wanda hakan abin daga hankali ne kwarai.

” Yadda za a taimakawa mutane kasancewar ciki ya zama laruri kuma a ko’ina a yankunan karkara ba inda ba cibiyoyin lafiya kuma haihuwa tanzama dole yadda ka san za a mutu haka ake haihuwa kaga ko ba kowa keda shi ba duk matar da ta kai haihuwar nan kana tunani lallai ranta a hannun Allah ne bayan ga wahalar haihuwa ace sai ta nemo kudi ta bayar bayan ta haihu ma kuma ga magunguna da abincin da za a ci a rayu kaga abin a duba ne”.

Saboda da haka nake son kowa ne dan majalisa ya yi bakin kokarinsa a kan wannan kudiri kun dai ga irin yadda kowa ya yi shuru hankalinsa ya dawo kan maganar masu ciki da wurin haihuwa da na gabatar da kudiri a kai domin muhimmancinsa, kuma kunji a cikin kudirin na ce a kira ministan lafiya a tabbatar da cewa an samu mafita a kan wannan hali da ake ciki an samu mafita a kan wannan kuma.majalisa ta tambaye shi meye dalilin da yasa mata basa amfana da magani wajen haihuwa da bayan haihuwarsu ayi masa wannan tambayar kuma a tabbatar da cewa an samu mafita a kai.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.