Home / Labarai / Muna Bukatar Makarantar Koyar Da Kiwon Kifi A Nasarawa – Sanata Aliyu Wadada

Muna Bukatar Makarantar Koyar Da Kiwon Kifi A Nasarawa – Sanata Aliyu Wadada

 

Daga. Bashir Bello, Majalisa Abuja

 

Sanata Aliyu Wadada daga Jihar Nasarawa ya bayyana bukatar al’ummarsa na a sama masu da katafariyar makarantar koyon kiwon kifi domin bunkasa tattalin arzikin Jihar da kasa baki daya.

Kasancewar Jihar na da arzikin manyan Kogunan da suke da wadataccen ruwan da za a iya yin kiwon kifi na zamani idan aka samu ingantaccen ilimin dabarun kiwon kifi.

Sai dai Sanata Aliyu Wadada ya koka a game da batun karancin wutar lantarkin da ake fama da shi a halin yanzu

Idan babu wutar lantarki kusan komai ba zai yi aiki kamar yadda ake bukata ba hatta da wayoyin hannu na zamani da ke hannun jama’a za su zama wani abu daban saboda ko dai dai da turakin wayoyin hannun ma da ake da su ma ba za su yi aiki saboda ba wuta

” hatta Injunan Nika da ake kira Mai bante da ake amfani da shi a da can duk ya ta fi a yanzu sai lantarki kawai ya maye gurbinsa, sai ya yi tambaya game da masu sayar da Janareto inda ya yi tambayar cewa ko sun fi karfin Gwamnati ne da lamarin wuta ya zama wani abu daban

Sanata Wadada ya kuma yi kira da cewa ya dace su a matsayinsu na majalisa da kuma bangaren Zartaswa su zama yan uwa masu yin aiki tare domin kasa ta samu ci gaban da ake bukata duk inda dayan mu ya kauce sai a dawo da shi kan hanya a nuna masa ba haka abin yake ba.

About andiya

Check Also

An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

….Lukman Ya Daina Surutu, A bari Majalisa ta yi aikin ta Daga Imrana Abdullahi Shugaban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.