Home / Labarai / Dalilin Da Yasa Na Gabatar Da Kudirin Yi Wa Dokar Miyagun Kwayoyi Kwaskwarima Ne – Sanata Ali Ndume

Dalilin Da Yasa Na Gabatar Da Kudirin Yi Wa Dokar Miyagun Kwayoyi Kwaskwarima Ne – Sanata Ali Ndume

 

Daga, Bashir Bello, Majalisa Abuja.

 

 

Sanata Mohammed Ali Ndume ya bayyana kudirin da ya kawo a majalisar Dattawa da cewa ya na nufin ayi wa dokar safara da shan miyagun kwayoyi ne ingantacciyar kwaskwarimar da za ta dace sosai domin kasa ta ci gaba.

Sanata Ali Ndume ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a ofishinsa Jim kadan bayan gabatar da kudirin yi wa dokar miyagun kwayoyi kwaskwarima.

Sanata Ndume ya ce ya dace a samu hukunci kwakkwara kuma mai zafi a game da lamarin harkokin masu safara da sayar da kwayoyi a fadin tarayyar Najeriya, wanda saboda haka ne ma aka gabatar da batun yi wa tsarin kwaskwarima.

“Doka a shashe na Goma sha daya ta bayar da cewa duk wanda aka same shi ko ya na Sayarwa ko ya na sarrafa shi ko kuma Noma shi to, idan an kama shi an kaishi kotu shi ne daurin rai da rai. Tun da kuwa an kawo gyara ne suk da daurin rai da rai da ke cikin tsohuwar dokar amma sai karuwa kawai lamarin yake yi, saboda haka ne duk hukuncin da za a yi ya dace ayi shi mai kyakkyawa ayi shi mai zafi kuma duk kasashe irinsu Amerika,Taiwan da.

Saudiyya da yawa daga cikin kasashen nan don a tabbatar da cewa an yaki lamarin shi ne suka ce hukuncin sa shi ne  kisa. Shi ne na jawo hankalin yan majalisa yan uwana kuma mafi rinjaye suka amince, amma akwai wadanda ba su amince ba, amma shi shugaban majalisa ya yanke hukunci a kan batun zabe na murya da muka yi,mu da muke cewa ayi hukuncin kisa ma duk mai sayar da kwaya ko duk wanda aka kama shi ya na shigo da kwaya ba ma wanda yake amfani da kwayar ba fa. Wanda yake yi ko ya na Nomawa shi ne hukuncinsa kisa, kuma ba wai munce ayi kisan nan don kawai muna son a kashe mutane ba don kawai ya hana ma mutane su aikata laifin ne kawai tun da dai ka san hukuncinsa, in ka aikata fa hukuncin kisa ne kawai sakamakon abin da ka aikata. Amma a yadda yake a yanzu abin sai karuwa kawai yake yi don haka ina ganin duk mai kishi da son kasar nan zai goyi bayan wannan matakin da muka dauka”.
A game da batun mafi akasarin masu yin amfani da wadannan miyagun kwayoyin manyan mutane ne ko yayan manyan mutane ne , ko, kana ganin wannan dokar za ta tsallake kuwa, sai Sanata Ali Ndume ya kada baki ya ce ai wannan fa an tsallakar da ita tuni a yau, kuma manyan mutanen ba sanatocin ba ne hakan ta sa na ce duk wadanda ke cewa kada ayi kisa to, ma’am akwai hannunsu a ciki ko suna da wani abin da za su boye kuma ni ina da yaya Goma da jikoki guda Ashirin”.
Hakazalika a game da batun sai an kai dokar matakin Jihohi domin su amince kuwa, Sanata Ndume ya ce, sam ba haka batun yake ba, ” ni na daukarwa kaina cewa kafin a gama ai an raba majalisar kashi biyu wadanda ke goyon bayan dokar su tashi wadanda kuma suke goyon bayan yan kwayar su tashi, duk wanda baya goyon bayan ayi daurin rai da rai lallai ya na da hannu a ciki kenan ko? duk mai cewa baya son ayi hukuncin kisa in dai ya na da kishi saboda da me zai fadi hakan domin su wadannan mutanen suna kashe mutane kuma.

Kuma Sanata Ndume ya ce batun aiwatarwa ba zai zama wani shakaki ba koda majalisar ta yi wannan dokar, musamman a yanzu da ake da shugaban NDLEA wanda tsayayyene mutum ne da shi ya kawo wadannan gyare gyaren a kan dokar, to, ai ba zai iya yin fafutukar ba idan ba a bashi goyon baya ba, maye ma matsalar cewa a kashe wanda yake kashe mutane.

About andiya

Check Also

Gwamna Dauda Lawal Ya Kaddamar Da Manyan Ayyuka A Bakura Da Maradun

A ci gaba da gudanar da bukukuwan cika shekara ɗaya a karagar mulkin jihar Zamfara, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.