Home / News / DALLATUN SHINKAFI,ZAMFARA NE SHUGABA A HALIN YANZU – SARKIN SHANU

DALLATUN SHINKAFI,ZAMFARA NE SHUGABA A HALIN YANZU – SARKIN SHANU

….DALLATUN SHINKAFI,ZAMFARA YA ZAMA FITILAR HASKEN

 

 

IMRANA ABDULLAHI KADUNA

 

 

 

DALLATUN SHINKAFI,ZAMFARA YA ZAMA FITILAR HASKEN SHUGABANCI
IMRANA ABDULLAHI KADUNA
An bayyana Mahmuda Aliyu Shinkafi da cewa UMAR shinkafi ya ta fi amma ya bar mana jigo wanda a halin yanzu wannan jigon shi ne shugaban al’umma baki daya.
Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi Sarkin Shanun Shinkafi na farko, ya bayyana hakan a wajen babban taron walimar murnar bikin Auren diyar Dallatu da aka yi a Kaduna.
Duk inda dan asalin Shinkafi yake bashi da shugaba sai Dallatun Shinkafi kuma Dallatun Zamfara sabida ya yi mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara na tsawon shekaru Takwas kuma ya yi Gwamnan Jihar Zamfara na tsawon shekaru hudu, saboda haka batun shugabanci ya tabbata a gare shi ba tare da wata tantama ba, “saboda haka ba mu da jagora sai shi”.
“Muna nan a kan akidarsa domin a kan Akidar marigayi Umaru Shinkafi yake saboda haka za mu ci gaba da binsa a koda yaushe”.
Jihar Zamfara baki daya na bukatarsa, domin abin bukata ne ga kowa.
Da yake tofa albarkacin bakinsa Alhaji Mahmuda Aliyu addu’a ya yi wa Sarkin Shanu da cewa Allah ya saka masa da alakairinsa
Tun lokacin da aka fito an samu nasarori kwarai kuma muna addu’ar Allah ya Sanya wa wannan Aure albarka.
Shinkafi Allah ya albarkace mu da jama’a iri iri da yawa musamman kamar irinsu Sarkin Shanu don haka muna yi wa Allah godiya.
Akwai kyaututtukan riguna ga Muhammadu Banas Shinkafi, Muhammadu Dan Ayya, Alhaji Bala Gora,Yahaya Katuru, Alhaji Abu Mai Dussa.
Dallatu ya ci gaba da cewa Allah ya ba mu albarkar da ke ciki, kuma ina yi wa Sarkin Shanu addu’ar fatan alkairi da taimakon Allah madaukakin Sarki.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.