Home / Labarai / Dan Majalisar Dandume Ya Jajantawa Mutanen Da Barnar Ruwa  Ta Shafa A Mahuta

Dan Majalisar Dandume Ya Jajantawa Mutanen Da Barnar Ruwa  Ta Shafa A Mahuta

 

Daga Imrana Abdullahi
Dan majalisar dokokin Jihar Katsina mai wakiltar karamar hukumar Dandume Honarabul Yahaya Nuhu ya bayyana alhininsa game da irin abin da ya faru na iftila’in Barnar ruwan sama da Iska da ya shafi mutanen Mahuta da ke karamar hukumar.
Honarabul Yahaya Nuhu ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da wakilin mu ta wayar Salula
Yahaya Nuhu ya ce hakika lamarin babu dadi ko kadan a kan irin abin da ya faru don haka nake jajantawa da kuma nuna Alhini a game da lamarin.
” na yi wani yunkuri inda na shaidawa mukaddashin Gwamnan Jihar Katsina wato mataimakin Gwamna da ke riko a halin yanzu kasancewar Gwamnan baya nan, Kuma nan da nan tuni har an bayar da umarni ga hukumar bayar da agaji ta Jiha da shugaban karamar hukumar Dandume da su je domin tantance abin da ya faru domin sanin abin da Gwamnati za ta yi a kan faruwar lamarin”.
Sabida haka “ina mika sakon jaje ga wadanda lamarin ya shafa sanadiyyar wannan ruwa da iska”
Kamar dai yadda muka rika gani a kafafen Sada zumunta na yanar Gizo daga garin Dandume mun ga hotunan yadda bishiyoyi sula fadi, gine gine kuma suka rushe wasu kuma aka yaye masu kwanan rufin gidajen da dai sauran su.
Fata dai Allah ya kiyaye ci gaba da faruwar hakan nan gaba.

About andiya

Check Also

RE: ALLEGATION OF EXTORTION BY OFFICER OF THE NGERIA CUSTOMS SERVICE FEDERAL OPERATIONS UNIT ZONE ‘B’ AT MOKWA AXIS OF NIGER STATE

      (1) The Comptroller Federal Operations Unit Zone ‘B’ Kaduna, Comptroller Dalha Wada …

Leave a Reply

Your email address will not be published.