Home / Kasuwanci / DANGOTE NE YA FI KOWA SAMA WA JAMA’A AIKIN YI A AFIRKA – WAYA

DANGOTE NE YA FI KOWA SAMA WA JAMA’A AIKIN YI A AFIRKA – WAYA

DAGA IMRANA ABDULLAHI

Alhaji Abdussalam Waya,Janar Manaja ne mai kula da harkokin Ssyarwa da kuma talla na kamfanin Matatar Sukarin Dangote, ya bayyana Dangote a matsayin wanda ya fi kowa sama wa jama’a aikin yi da suke dogaro da kawunansu.

Kamfanin Dangote ya zuba jarinsa a fannoni da dama da yake samar da kayayyakin da jama’a ke amfana kuma zai ci gaba da bunkasa harkokin ciniki da masana’antu domin kara karfafa tattalin arzikin nahiyar Afirka baki daya.

Abdussalam Waya ya bayyana hakan ne a wajen bikin ranar kamfanin Dangote da aka yi a kasuwar duniya ta Kaduna.

Waya, ya kuma shaidawa jama’a cewa kamfanin Dangote wuri ne da ake samun damarmaki masu tarin yawa da kowa zai iya samu ya amfana.

“Akwai gidauniyar Aliko Dangote da ke kokarin taimakawa al’umma a fannoni daban daban na rayuwa kuma ana amfana da dukkan abubuwan da suke aiwatarwa domin inganta rayuwar”.

Kamfanin na Dangote ya kuma yi alkawarin karin samar da damar zuba jari ga yan Najeriya.

Kamfanin Dangote zai samar wa dukkan dan Najeriya da ke bukatar zuba jari damar yin hakan da nufin kara bunkasa tattalin arzikin Najeriya da nahiyar Afirka baki daya.

Janar Manajan mai kula da harkokin Sayarwa da tallar kayan kamfanin Suga na Dangote, Abdussalamu Waya, ya bayyana masu shirya kasuwar baje kolin kasa da kasa da ke Kaduna a matsayin jajirtattun mutane a kokarinsu na bunkasa tattalin arzikin kasa, saboda haka sun cancanci a yi masu jinjina.

“Kasancewar kamfanin Dangote wanda ya fi kowa sama wa jama’a aikin yi, bayan Gwamnatin tarayya, kamfanin Dangote zai ci gaba da kara inganta kayayyakinsa da nufin samar da tattalin arziki mai karfi da zai bayar da damar tserewa tsara a duniya baki daya.

Waya, ya kara da bayanin cewa taken kasuwar na ba na “karawa kaya inganci” ya yi dai dai da irin kokarin kamfanin Dangote saboda kamfanin na fitar da Sumunti zuwa kasashe Goma Sha Biyar (15) a Afirka.

Ya ce “kamfanin Dangote na yin aikin hadin Gwiwa tare da Gwamnatin Jihar Kaduna a fannoni da dama domin inganta rayuwar jama’a”.

Tun da farko, da yake gabatar da jawabi mataimakin shugaba na biyu na kasuwar duniya ta Kaduna, Alhaji Faruk Suleiman, a jawabinsa na maraba godiya ya yi wa kamfanin Dangote bisa yadda yake taimakawa tsawon shekaru.

Ya ce duk da irin kalubalen da ake fuskanta a kasa, amma dai ana ci gaba da gudanar da ayyukan da aka saba a kasuwar ba tare da gajiyawa.

Ya ci gaba da bayanin cewa an zabi taken kasuwar na Bana ne domin irin yadda ake ta karkata zuwa ga bunkasa harkokin Noma da ma’adinai da ke bukatar a bunkasa su domin karin ingantawa.

A wajen ranar bikin kamfanin na Dangote dai sun baje kolin kayayyakin da kamfanin ke samarwa da suka hada da Takin Zamani,Sukari,Gishiri,Sumunti da motar kiran Sinotruck da kamfanin yake hadawa da sauran kayan kamfanin.

Bugu da kari shugabannin kamfanonin sumunti Friday Oligie, na Takin Zamani Mista Isiac Abana, Gishiri da kayan Dandanon Girki Solomon Adeoye duk sun yi wa jama’a jawabi da kuma na Sikari wanda Abdussalam Waya ya yi wa jama’a bayanin yadda kayan suke da yawan abin da suke samarwa.

A wani bincike da aka gudanar kusan babu gidan da ba a amfani da kayan kamfanin Dangote kama daga masu yin abinci, aikin Gona da harkokin Gini

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.