Shahararren dannkasuwa Alhaji Aliko Dangote ya tallafawa Gwamnatin Jihar Kano da motar Gwaje gwajen marasa lafiya ta tafi da gidanka da ke da karfin duba mutane dari 400 a kowace rana.
Da wannan motocin za a samu yi wa jama’a aikin Gwaji cikin sauki a Jihar Kano.
Indai ba a manta ba Jihar Kano na daya daga cikin Jihohin da suke fuskantar matsananciyar barazanar cutar Covid- 19 da ake kira da Korona bairus.