Home / Labarai / Dankishin Kasa Ya Daura Tutar Najeriya A Kan Gidansa

Dankishin Kasa Ya Daura Tutar Najeriya A Kan Gidansa

Mustapha Imrana Abdullahi
Wani dan kishin kasa da ke zaune a cikin garin Kaduna arewacin tarayyar Najeriya ya bukaci al’ummar kasar da su rika Sanya batun kishin kansu da kasarsu a gaba a koda yaushe domin komai ya kara inganta.

Mai kishin kasar ya ce saboda irin kishin da yake yi wa kasarsa ta haihuwa  ya sa ya Daura tutar Najeriya a kan gidansa da nufin kowa ya ga misalin yadda ake bayyana kishin kasa a wasu kasashen duniya da suka ci gaba.
“Na halarci wadansu kasashe a duniya kuma na ga irin yadda jama’ar kasar ke nuna kishin kasa ta hanyar Daura tutar kasar a kan gidajensu wanda hakan na nuni da kishin kasarsu a fili, saboda haka ne muke kokarin nunawa jama’a domin kowa ya dauki sahun yin hakan”, inji dan kishin kasan.
Za a dai iya ganin hoton gidan da ke dauke da tutar Najeriya kamar yadda yake a hoton gidan.

About andiya

Check Also

Jam’iyyar PDP Ta Taya Tsohon Gwamna Makarfi Murnar Ranar Haihuwarsa

…Sun Ce Shugaba Ne Abin Koyi,Mai Kokarin Hada Kan Al’umma Jam’iyyar PDP ta kasa ta …

Leave a Reply

Your email address will not be published.