Home / Big News / Dokta Suleiman Shinkafi Ya Tsaya Takarar Dan Majalisar Jihar Zamfara

Dokta Suleiman Shinkafi Ya Tsaya Takarar Dan Majalisar Jihar Zamfara

Daga Imrana Abdullahi
Shahararren dan Gwagwarmayar kare hakkin dan Adam Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya sayi fom domin tsayawa takarar dan majalisar dokoki na Jihar Zamfara domin wakiltar karamar hukumar Shinkafi.
In dai za a iya tunawa Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, mutum ne da ya dade ya na fafutukar ganin jama’a sun samu yancin kansu musamman ma daga mutanen da suke daukar kansu a matsayin wadanda su sun fi kowa a tsakanin al’umma.
Kamar dai yadda masu bibiyar irin yadda Dokta Suleiman Shinkafi ke gudanar da ayyukansa sun sani cewa babu wani mutum da ke kokarin fadakar da Gwamnati da kuma jama’a a game da irin yadda lamarin ke faruwa kan matsalolin tsaron da ake fama da shi a jihar Zamfara.
Saboda akwai wani lokaci can baya zamanin mulkin marigayi shugaba Buhari da Dokta Suleiman Shinkafi ya shiga kafafen yada labarai ya yi magana a game da halin rashin tsaron da ke faruwa a Jiharsa, lamarin da ya haifar da hatta marigayi shugaban kasa Buhari ya aiko da tawaga domin a tabbatar ko abin da Suleiman Shinkafi ya fadi gaskiya ne ko ya lamarin yake amma duk sai Gwamnatin ma ta gano cewa ma ya taimake ta ne game da batun lamarin tsaro.
Muna ganin cewa ma matsayi da aikin Dokta Suleiman Shu’aibu ke da shi ya wuce majalisar Jiha domin ya dace ne ya ta fi inda ake gwagwarmaya sosai a kasa baki daya, ya ci gaba da kwato yancin Jihar Zamfara baki daya.

About andiya

Check Also

TARON APC A ZAMFARA: Gwamna Lawal Ya Tabbatar Da Cewa Ƙarfin Gwamnati Na Rataye Ne Da Kyawawan Tsare-tsaren Jam’iyya

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada cewa nasara da ɗorewar kowace gwamnati na …

Leave a Reply

Your email address will not be published.