Home / Ilimi / Domin daidaito, adalci, Gwamna Radda ya amince da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ta kasance a Funtua

Domin daidaito, adalci, Gwamna Radda ya amince da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ta kasance a Funtua

 

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya karbi bakuncin tawagar hadin gwiwar al’ummar Funtua (Community-based Organisation) domin ziyara ta musamman a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli, 2023, a masaukin Gwamnan Jihar Katsina dake Birnin Tarayya Abuja.

 

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun Isah Miqdad, babban mai bayar da shawara a Ofishin Daraktan Yada Labarai.

 

Da yake jawabi a madadin tawagar, Alh. Umar Faruq Mutallab ya taya gwamnan murnar rantsar da shi a matsayin zababben gwamnan jihar Katsina na 5 bisa tafarkin dimokuradiyya. Ya kuma yaba masa bisa ga manyan nasarorin da ya yi wajen kafa kwakkwaran ginshikin da zai tabbatar da samun nasarar aiwatar da tsare-tsaren da suka shafi jama’a da inganta walwala da zamantakewar al’ummar jihar Katsina.

Bugu da kari, ya bayyana cewa sun zo Abuja ne domin neman sa hannun sa wajen kafa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Tarayya a Funtua wanda a cewarsa, zai tabbatar da kudurinsa na cika alkawuran da ya dauka na tafiyar da gwamnati mai dunkulewa ta hanyar tabbatar da adalci ga daukacin al’ummar jihar. Ya kuma bayyana cewa Funtua hedikwatar shiyyar Katsina ta Kudu ce kuma muhallinta na da dimbin al’umma da kuma makarantu masu kyau da za su iya ciyar da jami’ar da ake magana a kai.

Gwamna Malam Dikko Radda a nasa jawabin, ya bayyana cewa, domin samun daidaito, adalci, zai yi duk abin da ya dace bisa ga buri na doka domin ganin jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Gwamnatin Tarayya ta kasance a garin Funtua. Ya kuma kara da cewa Funtua ta taka rawar gani a tarihi da cigaban jihar Katsina. Bayan wani lokaci, Funtua ta zama cibiyar kasuwanci mai wadata; ta kuma yi fice a harkar noma da sauran ayyukan al’adu. A karshe ya yaba da shirin Kwamitin na samar da wurin wucin gadi da jami’ar za ta fara aiki da kuma samar da wurin dindindin da za a mika wa gwamnatin tarayya.

Tawagar sun hada da Alh. Umar Faruk Mutallab, Sanata Muntari Dandutse, Hon. Musa Adamu Funtua, Alh. Lawal Garba, Alh. Amadu Ardo, Dr Amiru Sanusi, Mambobin Majalisar Wakilai na Musawa/Matazu, Funtua/Dandume and Malumfashi/Kafur. Hakazalika, ‘yan majalisar dokokin jihar Katsina masu wakiltar kananan hukumomin Danja, Dandume, Funtua, da Faskari na cikin tawagar. Haka kuma shugabannin Funtua, Faskari, Dandume, Musawa, Matazu, Danja, da Bakori suma sun halarci taron.

 

 

 

About andiya

Check Also

Edo 2024: Group Hold Symposium In Support Of Asue Ighodalo

  The Good Governance Advocacy Group, has held a symposium to drum their support for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.