Home / Labarai / Duk Inyamurin Da Ke Maganar Biyafara Karya Yake – Yakubu Biyafara

Duk Inyamurin Da Ke Maganar Biyafara Karya Yake – Yakubu Biyafara

Imrana Abdullahi

Alhaji Yakubu Biyafara ya bayyana cewa duk wani Inyamurin da ke maganar Biyafara karya kawai yake akwai dai wani abu daban da yake bukatar a haifar kawai, domin kamar yadda mutumin da ake wa lakabi da Yakubu Biyafara ke cewa tuni aka sha ruwa aka binned rijiya.

Alhaji Yakubu Biyafara ya dai bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyon da ya aikawa manema labarai.

Alhaji Yakubu ya ci gaba da cewa ya dace kowane Inyamuri fa ya Sani cewa a zamanin ana Yakin Biyafara da wahala ta kai wa Inyamurai iya wuya sun rika yin wata waka su na cewa “Allah ka cece mu, kaji tausayi mu domin salwantar ran ya yi yawa”, sai a yanzu wani Inyamuri zai kara kawo ma kansa wata matsalar da ya yi fama da ita shekaru da yawa a can baya?

Ya dace wadannan yara da ke kururuwar Biyafara su tambaya shin me ya sa a shekarar 1969 da Ojuku ya ce zai yi kirsimati a Fatakwal, amma sai ga shi ya gudu kasar Abirikost ya kuma cewa Ifiyon ya yi saranda shi ya gudu , don haka wadannan yaran su Sani cewa lokacin da aka yi yaki a can baya su ba a haife su ba ma saboda haka a sake tunani kawai.

“Ni ba da su ma nake magana ba saboda ku san dukkansu ba a haifesu ba lokacin da aka yi wancan Yakin na basasa da Inyamurai suka kwashi kashinsu a hannu, har suka kirkiro da wakar Allah ya cece su ya duba halin da suke ciki.

“Kuma a nan kasar mu sa idanu mu gani sai an kira Inyamuri a tambaye shi kai Inyamuri ne ya ce ni ba shi ba ne Musa idanu mu yi kallo, domin ni na san illar Inyamuri saboda shi ne kawai yake kiran kansa daga ni kafin kai wato koda yaushe shi ne a gaban kowa wato “I before you”, duk inda suke kirarinsu kenan, saboda haka nake kira ga daukacin Inyamurai su sake tunani.

“Ni idan zan yi magana da wani Inyamuri zan yi ne da mutane irinsu “Ofara da Akanu Ifiyon”, amma ni ko irinsu Rochas Okorocha sun yi Mani kan kanta in yi magana da su game da sanin da na yi wa Inyamurai a Najeriya.

“Su bincika waye ya sayar da yankin Bakassi a shekarar 1962 da aka zo ana neman yankin Kamaru ta Gabas, kafin su yi wata magana, ai mun san wanda ya karbo yankin Sardauna, amma wa ya sayar da yankin Bakassi?

Ya kara da cewa nan gaba kadan zan gayawa duniya ko waye Inyamuri ma domin kowa ya san shi sosai.

About andiya

Check Also

Union Across River Niger: New Nigerian Editor Brother’s Wedding Grounds Makurdi

    Makurdi the capital of Benue State was agog all through the weekend, as …

Leave a Reply

Your email address will not be published.