Home / Labarai / DUK WANDA BA SHI DA KATIN ZABE BA ZA A YI MASA RAJISTA BA ‘ MUNKAILA HASSAN TELA

DUK WANDA BA SHI DA KATIN ZABE BA ZA A YI MASA RAJISTA BA ‘ MUNKAILA HASSAN TELA

 

DAGA IMRANA ABDULLAHI

Munkaila Hassan Tela Bazumbo Jagaban kungiyar Zabarkano a Najeriya ya bayyana cewa duk dan kungiyarsu da bashi da katin zabe ba za su yi masa rajista a matsayin dan kungiyar Zabarkano.

Munkaila Hassan Tela ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron Rantsar da shugabanni na kasa da kuma na Jihohi na kungiyar Zabarkano a Najeriya.

Munkaila Hasan ya ci gaba da bayanin cewa su a matsayinsu na kungiyar Zabarkano masu son ciyar da kasa tare da al’ummarta gaba shi yasa suka Sanya dokar cewa duk wanda ke son ayi masa rajista a matsayin dan kungiya, ya zama dole ya nuna katin zabensa da katinsa na dan kasa domin su tabbatar da cewa wannan garanti ne ba bakunci yake ba.

“Hakika mu a kungiyar Zabarkano mun dade muna bayar da gudunmawar mu wajen ci gaban kasa don haka muke yin gargadi ga dukkan mambobinsu da du rika bin doka da ka’ida a ko da yaushe, saboda haka muke bin tsarin cewa kada kowa ya shigo mana da harkar siyasa a cikin kungiyar Zabarkano amma mutum zai iya yin siyasarsa a inda duk yake ba tare da saka kungiya cikin lamuran siyasa ba”.

Wannan dalili ne yasa yayan kungiyar Zabarkano suka taru a garin Abuja domin kaddamar da shugabanni na kasa daga Jihohi 36 da Abuja, wanda idan wani al’amari ya faru a wani wuri zamu iya kiran shugabannin wannan Jiha mu ce masa yaje domin ya ga me ya faru ga dan uwanmu.

“Idan wani abu ya aikata na karya dokar Najeriya to, hakika bashi daga cikin mu. Haka kuma abin da zai kawo fitina kamar satar mutane ko fashi da Makami hakika bashi daga cikin mu.Amma idan ba irin wadannan manyan laifuka ba to, zamu iya zuwa kuma mu nema masa alfarma, mu san yadda za a yi larurar ba tare da an dauke shi Bako a wannan kasa ba, saboda mukan samu wadansu abubuwan da idan abu ya faru da Bazabarme sai ace shi ba dan kasa bane duk da cewa ga takardu ga komai ga kuma garuruwanmu wanda tun kafin shekarar 1914. Domin akwai wani kauye da ake cewa Bankanu a Kudancin Sakkwato ya girmi garin Sakkwato kuma Zabarmawane wannan kenan.

“Kowane shugaba an bashi takardarsa ta shaidar cewa shi ne shugaba a wannan Jihar don haka sai ya tabbatar da hadin kai tsakaninsu Zabarmawa don a taimakawa Gwamnati”, inji Munkaila Hassan Tela.

Ya kuma yi kira ga daukacin yayan kungiyar na kasa cewa muna son koda akwai wani sabani da dan uwanka na bayan fage, kada ka sake ka kawo shi a cikin kungiya ku tsaya can kuyi larurarku ku kammala ta can ko kuma idan larurar kungiya ta taso a hada kai aga cewa wannan abin da ake buri na taimakon kai da kai da taimakon kasa Najeriya ya cika.

“A kuma rika yin hakuri da Juna a guji abin da Gwamnati bata so, ba mu fata ko son wani ko wasu Zabarmawa su kasance a cikin wata kungiyar da ba mu bukata sam sam ko kuma shiga kungiyar asiri ko abin da ya sabawa dokar kasa lallai ba mu bukatar hakan, kuma daman an san mu jajirtattu muke wajen neman abin kan mu na hakkin mu bakin Gwargwado “.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.