Related Articles
Imrana Abdullahi
Daya daga cikin makusantan shugaban tarayyar Nijeriya Malam Mamman Daura ya bayyana cewa duk maganganun da wadansu mutane ke yi masa ba gaskiya bane.
Mamman Daura ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta bbc hausa.
Mamman Daura ya kuma ce tun a lokacin marigayi Sardaunan Arewa ya zabe su suka je karatu kasar Ingila, kuma game da batun cin hanci kuwa Malam Mamman Daura ya ce daman can akwai shi koda yaushe tun tale tale.
“Ai baka yi wa Gwamnati kazalandan, ko shawara ce sai an tambaye ni, amma ba haka kawai ba, kuma shekaru sama da Arba’in muna tare da marigayi Abba Kyari tun da muka yi aiki tare da shi a kamfanin jarida na New Nigeria, kuma shi yana cikin Gwamnati ni kuma ina daga waje ne ba kamar yadda ake yin Zargi ba”.
Mamman Daura ya kuma tabbatar da cewa kokarin marigayi Malam Abba Kyari ne yasa aka samu kamfanonin hada Taki 31 kusan dukkan wannan tashin kamfanoni kokarinsa ne.
Shi kuma Marigayi Alhaji Sama’ila Isa Funtuwa suna tare da shi shekaru 40 kenan kuma sun hadu ne tun a lokacin suna aiki a masakar UNTL da ke garin Kaduna, lokacin marigayin yana matsayin shugaban kula da ma’aikata na kamfanin UNTL, ni kuma ina Darakta tun daga nan muka saku kwarai, har muka je muka kafa masakar Funtuwa duk muna tare har rasuwarsa don haka rasuwar mutanen nan biyu ya kidimani kwarai domin naji a jikinsa sosai.
Mamman Daura ya ci gaba da bayanin cewa shugaba Buhari Kawunsa ne domin kanin mahaifinsa ne, to, ta yaya za a rika yada irin maganganun da ake yi?
Kuma a lokacin da ake yi wa wani hukuncin cin hanci koda kashe wanda ya yi shi aka yi a lokacin ne zaka ga wani kuma ya kara aikata laifin don haka daman can akwai batun cin hanci da karbar sharawa.